An umarci shahararren mawaƙin Amurka D4vd, wanda ainihin sunansa shi ne David Anthony Burke, da ya fuskanci shari’a kan zargin kashe Celeste Rivas Hernandez mai shekaru 14. Wata kotu a Los Angeles ta yanke hukuncin cewa masu gabatar da ƙara sun gabatar da isassun hujjoji da za su ba da damar ci gaba da shari’ar.
Masu gabatar da ƙara na zargin cewa Burke ya kashe Rivas Hernandez a watan Afrilun 2025, bayan da yarinyar ta yi barazanar bayyana wasu bayanai game da dangantakarsu. An gano gawarta bayan wasu watanni a cikin ɓangaren gaba na wata mota kirar Tesla da aka yi rajista da sunan Burke.
Burke na fuskantar tuhume-tuhume da suka haɗa da kisan kai na mataki na farko, cin zarafin yarinya ta hanyar lalata da kuma lalata gawar ɗan Adam ba bisa ƙa’ida ba. Masu gabatar da ƙara sun gabatar da wasu hujjoji da suka haɗa da bayanan binciken ƙwararru, DNA, hotuna da saƙonnin da suka ce suna da alaƙa da lamarin.
Sai dai Burke ya musanta aikata laifin kuma ya ce ba shi ne ya kashe yarinyar ba. Lauyoyinsa sun kuma bayyana cewa hujjojin da aka gabatar ba su tabbatar da cewa shi ne ya aikata kisan ba.
Hukuncin kotun na nufin cewa yanzu shari’ar za ta ci gaba zuwa gaban alkalai da za su saurari cikakken bayanin lamarin. An tsara Burke ya sake bayyana a gaban kotu a ranar 31 ga Agusta, yayin da ake sa ran shari’ar za ta iya fara gudana cikin makonnin da za su biyo baya.