An Shekaru 4 Da Kotu Ta Yankewa Abdulmalik Tanko Mai Shekaru 38 Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Laifi Sacewa Da Kashe Hanifa.
Hanifa Abubakar (an haife ta ranar 5 ga Afrilu, 2016). Abdumalik Tanko, mamallakin makarantar Noble Kids Academy da ke karamar Nassarawa cikin jihar Kano, ya yi garkuwa da ita, kuma ya kashe ta. Lamarin dai ya dauki hankalin al’ummar kasa saboda karancin shekarun wacce aka kashe da kuma yadda aka yi sanadin mutuwar ta.
Mai Shari'a Usman Na'abba da ke jagorantar ƙarar ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis 28 ga watan Yulin 2022. Ana zargin malaminta Abdulmalik Tanko ne ya sace ta a watan Disambar 2021 tare da kashe yarinyar mai shekara biyar.
Sannan kotu ta sami Hashimu Isyaku da laifin hada kai wajen kisan Hanifa da ɓoye laifin aikata garkuwa da Hanifa, sannan yana da masaniya an yi garkuwa da Hanifar. Sannan kotu ta wanke Fatima Jibril daga zargin rubuta wa iyayen Hanifa wasikar sanar da su an yi garkuwa da ita. Sai dai ta same ta da laifin hannu waje yin garkuwa da Hanifa, da masaniyar an yi garkuwa da ita.
Kotu ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin garkuwa da Hanifa da ɗaurin shekaru biyar a gidan gyaran hali na garkuwa da mutum.
Kotu ta yanke wa Fatima hukuncin shekara biyu a gidan gyaran hali kasancewarta uwa. Ta kuma yanke wa Hashimu hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan gyaran hali sannan daga baya a kashe shi.
Kisan Hanifa ya ja hankalin duniya inda dubban mutane, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, suka yi tur da shi.
