Farashin Siminti A Najeriya Ya Ninka Na Kasashen Afirka Da Dama Duk Da Yawaitar Samarwa

Duk da cewa Najeriya na da ƙarfin samar da siminti sama da tan miliyan 60 a duk shekara, wanda ya sanya ta cikin manyan ƙasashen Afirka masu kera siminti, har yanzu 'yan ƙasar na sayen siminti a farashi mafi tsada idan aka kwatanta da ƙasashe da dama na nahiyar.
A kasuwannin Abia, Abuja da Legas, buhun siminti mai nauyin kilo 50 na sayuwa tsakanin Naira 12,500 zuwa N15,000, yayin da irin wannan buhu ke sayuwa tsakanin N6,000 zuwa N7,000 a Afirka ta Kudu, N4,000 zuwa N5,000 a Masar, N6,500 zuwa N7,500 a Kenya, sannan N7,000 zuwa N8,000 a Ghana.
Masana'antar siminti ta Najeriya ta fi karkata ne ga manyan kamfanoni uku, wato Dangote Cement, BUA Cement da HBM Nigeria Plc (tsohon Lafarge Africa), waɗanda ke da ƙarfin samar da tan miliyan 60 zuwa 65 a shekara. Ana kuma sa ran wannan ƙarfin zai kai kusan tan miliyan 85 idan sabbin masana'antu da ake ginawa suka fara aiki.
Duk da haka, yawan simintin da ake amfani da shi a cikin gida bai wuce tan miliyan 25 zuwa 30 a shekara ba, abin da ke nuna cewa ƙasar na samar da fiye da bukatarta tare da fitar da ragowar zuwa ƙasashe maƙwabta.
Rahotanni sun nuna cewa Dangote Cement kaɗai na samar da fiye da rabin simintin da ake kerawa a Najeriya, inda ƙarfin masana'antunta ya kai kusan tan miliyan 35.3 a shekara. Ana sa ran wannan zai haura tan miliyan 41 bayan kammala sabuwar masana'antarta da ke Itori a jihar Ogun.
BUA Cement ita ce ta biyu wajen samar da siminti, tana da ƙarfin tan miliyan 17 zuwa 20 a shekara, yayin da HBM Nigeria Plc ke da ƙarfin tan miliyan 10.5.
Akwai kuma sabbin masana'antun da ake ginawa, ciki har da MSM Cement a Kebbi mai ƙarfin tan miliyan uku a shekara da Resident Cement a Bauchi da ake sa ran za ta samar da tan miliyan 10.
A shekarar 2025, kamfanonin siminti uku sun samu kuɗaɗen shiga sama da Naira tiriliyan 6.53, yayin da ribar da suka samu bayan haraji ta kai Naira tiriliyan 1.65, adadin da ya nuna ƙarin kashi 142 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Masu sukar lamarin sun ce irin wannan riba mai yawa na haifar da tambaya kan ko masu amfani da siminti a Najeriya na biyan fiye da abin da ya kamata, musamman ganin cewa ana samar da kayan ne a cikin gida.
Sai dai kamfanonin sun ce tsadar makamashi, cire tallafin mai, hauhawar farashin gas da dizal, faɗuwar darajar naira, tsadar shigo da kayayyakin gyaran injuna da kayan aiki, da kuma matsalolin sufuri ne ke ƙara tsadar samar da siminti.
Sun bayyana cewa kuɗin jigilar siminti kaɗai na iya kaiwa kashi 30 zuwa 40 cikin ɗari na farashin da mai amfani ke biya.
Haka kuma, kamfanonin sun ce ci gaba da buƙatar siminti wajen gine-ginen gidaje, hanyoyi da sauran ayyukan raya ƙasa na sa babu wani dalili da zai tilasta rage farashi.
A halin yanzu, Najeriya na fitar da siminti da clinker zuwa ƙasashe irin su Ghana, Kamaru da Nijar, lamarin da masana ke ganin yana rage matsin lamba na saukar da farashi a cikin gida.
Tsadar siminti ta fara yin tasiri ga ayyukan gwamnati. Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa gwamnati za ta fara tattaunawa da kamfanonin siminti domin nemo hanyar rage farashi, saboda hauhawar farashin na ƙara tsadar aiwatar da kwangilolin gwamnati.
Umahi ya kuma buƙaci kamfanonin su ƙara yawan samar da siminti domin tallafa wa manyan ayyukan raya ƙasa.
Masana sun kiyasta cewa Najeriya na fuskantar ƙarancin gidaje sama da miliyan 16, inda suka ce tsadar siminti na ƙara wahalar gina gidaje masu araha, makarantu da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Shugaban Ƙungiyar Masu Gina Gidaje ta Najeriya (REDAN), Oba Akintoye Adeoye, ya ce tsadar siminti na daga cikin manyan matsalolin da ke hana samar da gidaje masu sauƙin farashi.
Shi ma Daraktan Housing Development Advocacy Network (HDAN), Festus Adebayo, ya buƙaci gwamnatin tarayya ta samar da manufofin da za su rage kuɗin samar da siminti, ciki har da inganta samar da iskar gas, tabbatar da wutar lantarki mai ɗorewa, rage harajin shigo da muhimman kayan aiki da kuma ƙarfafa kafa sabbin masana'antun siminti domin samar da gasa a kasuwa.
Masana sun kuma ba da shawarar a inganta hanyoyin jirgin ƙasa zuwa manyan masana'antun siminti, a ƙarfafa sa ido kan farashi ta hannun Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya da Samar da Gasa (FCCPC), tare da buƙatar kamfanonin su riƙa bayyana bayanan yawan simintin da suke samarwa da farashin da suke sayarwa daga masana'antu domin inganta gaskiya da adalci a kasuwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post