Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da zabar mataimakinsa, Murtala Sule Galadima Garo, a matsayin abokin takararsa a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027.
Sanarwar ta fito ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.
A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taro na dabarun siyasa da naɗaɓɓun jami'an gwamnatin tarayya na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano da ke Abuja.
Gwamnan ya ce ya yanke wannan hukunci ne sakamakon biyayya, jajircewa da kuma ƙwazon da Garo ya nuna wajen ci gaban Jihar Kano tun bayan da ya hau kujerar mataimakin gwamna.
Ya kuma bayyana gamsuwarsa da yadda suke aiki tare, yana mai cewa Garo ya nuna ƙwarewa, sadaukarwa da kuma ɗaukar nauyi wajen gudanar da ayyukansa.
Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cikakken amincewarsa da mataimakin gwamnan, inda ya ce gudummawar da yake bayarwa ta ƙara ƙarfafa ƙoƙarin gwamnatin wajen samar da ci gaba mai ma'ana a faɗin Jihar Kano.
"Ina mai tabbatar muku cewa ban yi nadamar zaɓen Garo a matsayin mataimakina ba, kuma ya tabbatar da cewa shi ne wanda ya dace. Ina da cikakkiyar amincewa da shi," in ji gwamnan.
Haka kuma, Gwamna Yusuf ya buƙaci shugabannin jam'iyya, masu riƙe da muƙaman siyasa da magoya baya da su ci gaba da haɗin kai da jajircewa domin ci gaba da gina kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu tare da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027.
