Kasashen Tarayyar Turai Na Nazarin Kakaba Takunkumi Kan Kasuwancin Kayayyakin Da Ke Fitowa Daga Matsugunnan Isra'ila Da Ake Ganin Ba Su Halasta Ba

 Ƙasashen Tarayyar Turai (EU) na duba yiwuwar ƙaƙaba sabbin takunkumai kan kayayyakin da ke fitowa daga matsugunnan Yahudawa na Isra'ila da aka gina a yankin Yammacin Kogin Jordan (West Bank), waɗanda dokokin ƙasa da ƙasa ke kallon ba su da halacci.

Ƙasashen Tarayyar Turai (EU)

Ministocin harkokin wajen ƙasashen EU sun tattauna kan wata takarda da Hukumar Tarayyar Turai ta shirya, wadda ta gabatar da zaɓuɓɓuka uku: kafa tsarin ba da lasisin shigo da kayayyaki, kakaba haraji mai tsauri kan kayayyakin, ko kuma hana shigo da su gaba ɗaya.

An fara wannan tattaunawa ne sakamakon ƙarin matsin lamba daga wasu ƙasashen EU, waɗanda ke nuna damuwa kan ci gaba da faɗaɗa matsugunan Isra'ila da kuma tashin hankalin da ake samu a Yammacin Kogin Jordan. Hakanan, kotun International Court of Justice (ICJ) ta bayyana a shekarar 2024 cewa waɗannan matsugunan sun saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Sai dai duk da ci gaba da tattaunawar, jami'an EU sun ce ba a sa ran cimma matsaya ta ƙarshe nan take ba, saboda akwai sabanin ra'ayi tsakanin ƙasashe mambobi kan irin matakin da ya kamata a ɗauka da kuma tsarin doka da za a bi wajen aiwatar da shi.

A nata ɓangaren, gwamnatin Isra'ila ta ci gaba da musanta cewa matsugunan ba su da halacci, tana mai cewa tana da hujjojin tarihi da na tsaro kan ci gaba da gina su.

Post a Comment

Previous Post Next Post