Gwamnatin Jihar Katsina Ta Sake Ɗaukar Sabbin Ma’aikatan Malaman Makarantar Firamare 2,158 A Fadin Jihar
Ingantaccen ilimi yana farawa ne da ingantattun malamai. Shi ya sa tabbatar da tsarin ɗaukar ma’aikata na gaskiya da ya dogara da cancanta yana da matuƙar muhimmanci wajen gina makomar da muke gani wa ‘ya’yanmu da kuma Jiharmu ta Katsina.
A yau, na sami damar ƙaddamar da rabon takardun kama aiki ga sabbin malamai 2,158 da aka ɗauka na Ma’aikatar Ilimi ta Farko da Sakandare (SUBEB). An zaɓe su ne bisa cancanta, ƙwarewa, da kuma buƙatun ainihin ma’aikata da makarantunmu suke da su, domin tabbatar da cewa kowane yaro yana da kyakkyawar dama ta koyo daga hannun malamai ƙwararru masu sadaukarwa.
Tun daga farkon gwamnatinmu, mun ɗauki sama da malamai 9,000, mun kuma gyara makaratu da dama, mun gina sabbin wuraren koyo, mun horar da malamai sama da 25,000, mun ƙaddamar da tallafin malamai na karkara na N30,000, mun faɗaɗa koyo ta hanyar dijital ta hanyar raba na’urorin tablet 18,000, sannan mun kafa Cibiyar Horaswa da Bunƙasa Malamai. Waɗannan zuba jari ne da ke nuna jajircewarmu wajen sake ginawa da ƙarfafa fannin ilimi da haɓaka ci gaban mutane.
Ga sabbin malamai da aka naɗa, ina yi muku barka da wannan dama da kuka samu ta hanyar tsari mai tsauri da ya dogara da cancanta. Naɗin ku ba aiki ba ne kawai; kira ne na hidima. Ina ƙarfafa ku da ku riƙe da mafi girman matakin ƙwarewa, gaskiya, da sadaukarwa yayin da kuke tarbiyyantar da tunani da ɗabi’ar ƙarni na gaba.
A ƙarƙashin shirinmu na "Gina Makomarku", za mu ci gaba da zuba jari a fannin ilimi domin ci gaban ɗorewa na Jihar Katsina ya dogara ne da ingancin ilimin da muke bayarwa a yau.
Allah (SWT) ya albarkaci malamai, ‘ya’ya, da Jihar Katsina.