A wasan da aka fafata a cikin talatainin daren jiya Laraba, ƙungiyar Portugal ta samu nasarar doke Croatia bayan, da ta dawo cikin wasan tare da sake zura wata ƙwallon a mintina na 94 ana saura minti biyu a tashi wasan, ta hannun Goncalo Ramos.
A wasan na rukunin 'yan 32, ƙungiyar tawagar Croatia sun yi ƙoƙarin mayar da wasan ɗanye bayan da suka sake cin wasa a mintinan ƙarshe. Sai dai alƙalin wasan ya yi amfani da ƙwallon da aka yi amfani da ita a wasan, inda ta gano wani abu wanda da yawan 'yan wasan da ma masu kallo ba su lura da shi ba. Wato yadda wani ɗan wasan Portugal mai suna Renato Vega ya taɓa ƙwallon da kansa a ƙoƙarinsa na fitar da ƙwallon waje, wanda a daidai lokacin Mario Pasalic yana cikin satar gida. An gano hakan ne ya hanyar amfani da wata na'ura da aka dasa a cikin ƙwallon.
Daga ƙarshe dai alƙalin wasan ya kashe ƙwallon tare da bayar da shaidar cewa satar gida ce. Lallai da ba don wannan ball ɗin ba da wataƙila Portugal sai dai buzunta, domin lokacin mai horas da ƙungiyar ya gama cire duk wasu masu kyau a tawagar ta Portugal.