Birnin Kebbi – Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa matakin rufe makarantu a wasu sassan jihar ba ya da wata alaƙa da siyasa, sai dai an ɗauke shi ne domin tabbatar da tsaron rayuka da lafiyar ɗalibai da malamai.
Gwamnatin ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da tsaron ma’aikatan makarantu da ɗalibai a duk lokacin da suke gudanar da harkokin karatu.
Mai Bai wa Gwamna Nasir Idris Shawara na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Dabaru, Abdullahi Zuru, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Birnin Kebbi ranar Alhamis.
A cewarsa, ci gaba da rufe makarantu a yankunan da matsalar tsaro ta fi kamari ya zama wajibi domin kare rayukan ɗalibai da malamai.
“An ɗauki wannan mataki ne kimanin watanni bakwai da suka gabata saboda ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro.
“Rufe makarantun ba siyasa ba ce. Martani ne kai tsaye ga matsalar ‘yan bindiga da ke addabar Jihar Kebbi da ma yankin Arewa maso Yamma,” in ji Zuru.
Ya kuma zargi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da amfani da wasu ƙungiyoyi da ba a san ko su waye ba, tare da kafafen sada zumunta, wajen tunzura iyaye su nemi a sake buɗe makarantu nan take.
“Ba za a yi siyasa da tsaron rayukan OKyaranmu ba. Babu wata matsin lamba da za ta sa gwamnati ta yi sassauci kan kare rayukan ɗalibai.
“Jihar Kebbi ba ita kaɗai ba ce ke fuskantar wannan ƙalubale. Har yanzu akwai makarantu da ke ci gaba da kasancewa a rufe a Jihar Borno da wasu jihohin Arewa saboda daɗaɗɗiyar matsalar rashin tsaro,” in ji shi.