Wasu maza biyu ‘yan ƙasar Guatemala sun amsa laifinsu a wata kotun tarayya da ke jihar Texas, Amurka, bisa zargin hannu a wata babbar hanyar safarar baƙi ba bisa ƙa’ida ba da ta yi sanadin mutuwar mutane 55 a wani mummunan hatsarin motar dakon kaya da ya faru a jihar Chiapas ta ƙasar Mexico a shekarar 2021.
Waɗanda suka amsa laifin su ne Jorge Agapito Ventura, mai shekara 34, da Oswaldo Manuel Zavala Quino, mai shekara 26. Sun amince cewa sun yi haɗin gwiwa da wasu wajen safarar manya da ƙananan yara daga Guatemala ta cikin Mexico zuwa Amurka ba bisa ƙa’ida ba. An cunkusa sama da mutane 160 a cikin motar dakon kaya, wadda daga bisani ta yi hatsari ta bugi gada, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata fiye da mutum 100.
Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta bayyana cewa mutane biyar daga cikin mutum shida da ake tuhuma a wannan shari’ar sun riga sun amsa laifinsu. Ana sa ran za a yanke wa mutanen biyu hukunci a ranar 6 ga Oktoba, kuma kowannensu na fuskantar yiwuwar hukuncin ɗaurin rai da rai.
Jami’an shari’a sun ce wannan hatsari na daga cikin mafi muni da suka taɓa faruwa a tarihin safarar baƙi ba bisa ƙa’ida ba, suna mai jaddada cewa masu safarar mutane suna fifita riba fiye da rayuwar waɗanda suke safararsu. Hukumomi sun ce za su ci gaba da gurfanar da duk masu hannu a irin waɗannan laifuka domin tabbatar da adalci.