Wasikar Jaafar Jaafar Ga Shugabannin Nijeriya

Masu riƙe da madafun iko ku bi duniya a sannu. In mune yau, ba mune gobe ba. Kada ka ƙuntata wa wani don ka daɗaɗa wa gwamnati, domin gwamnati tamkar ‘zalunci’ take — ba ta dawwama. Duk gaskiyarka lokacin da kake rike da muƙamin gwamnati, in wata gwamnatin na so ta wulaƙanta ka za ta iya. 

Nasir El-Rufa'i

Ka duba shuhura da ƙarfin iko irin na Major Hamza Al-mustapha da Mohammed Abacha, amma da gwamnatin Obasanjo ta zo sai da suka shafe shekaru a gidan yari. 

Shin ba za ka hankalta da ƙasaita da ƙarfin iko irin na Sambo Dasuki da Bello-Adoke da Diezani Alison-Madueke da Stella Odua da Peter Godsday Orubebe da su Gordon Obua a lokacin mulkin Jonathan ba? Shin ba ka duba yadda suka ƙarke a lokacin mulkin Buhari ba? 

Shin ba za ka duba abin da ya faru da Godwin Emefiele ba ka hankalta? Mallam ka duba ƙasaita irin ta su Abubakar Malami da Hadi Sirika da Sale Mamman da Nasir El-Rufai a zamanin mulkin Buhari, yau ga shi su ne ke jewa daga kotu zuwa kurkuku. 

Alƙalin tirabuna ta CCT Danladi Umar ya yi sharafinsa lokacin yana kan ganiyarsa. Ya sa an gurfar masa duk wani babba da ke takun saƙa da gwamnati, ko kuma wani mutum da gwamnati ke son ta ga bayansa. An gurfanar da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da alƙalin alkalan Nigeria Justice Water Onnoghen a gabansa. Kai har Tinubu ya taɓa gurfana a gabansa. 

Danladi Umar bai taɓa tunanin za a iya cire shi ba ba bisa ƙa’ida ba, amma da yake gwamnati, gwamnati ce, rana tsaka aka yi wa doka karan tsaye, aka cire shi yana ji, yana gani, kuma yau an aike shi kurkuku. 

Masu rike muƙaman gwamnati, a bi duniya a hankali!

Jaafar Jaafar

Post a Comment

Previous Post Next Post