Hukumar EFCC A Nijeriya Ta Gurfanar Da Shugaban Miyetti Allah A Gaban Kotu

EFCC ta gurfanar da shugaban Miyetti Allah Bello Bodejo kan zargin almundahanar dala miliyan 2.33.

Bello Badejo

Hukumar EFCC ta gurfanar da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin almundahanar kuɗi da ta kai dala miliyan 2.33.

An gurfanar da Bodejo a gaban mai shari'a Inyang Edem Ekwo kan tuhume-tuhume guda 12 da suka shafi zargin karɓar makudan kuɗaɗen dalar Amurka ba tare da bin hanyar banki kamar yadda doka ta tanada ba.

Bodejo ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

Lauyan EFCC, Wahab Shittu (SAN), ya buƙaci kotu ta ci gaba da shari'ar tare da tsare wanda ake zargin, yayin da lauyan Bodejo, Ahmed Raji (SAN), ya nemi a ba shi beli.

Sai dai kotun ta ba da umarnin a tsare Bodejo a ofishin  EFCC, sannan ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 20 ga Yulin 2026 domin yanke hukunci kan buƙatar belinsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post