Nijeriya Ta Samu Wakilci A Bikin Binne Sheikh Ali Khamne'i

Da wayewar garin yau Alhamis 09/07/2026 an hango hoton tawagar shugaban Ƙungiyar Shi'a na Nijeriya Sayyid Sheikh Ibrahim Zakzaky yana sauka a filin jirgin ƙasar Iran domin halartar jana'izar jagoran Iraniyawan Ayatullah Ali Khamne'i wanda aka fara tsawon kwanaki da suka shuɗe.
Ƙasar Iran ta ware mako guda domin yin bikin jana'izar jagoran nasu, wanda aka zazzagaya da gawar tasa cikin manyan biranen ƙasar da ƙasashen maƙwabta na Shi'a, domin yin bankwana da gawar jagoran nasu, inda suka fara taron bankwanar a garin Tehran, an kuma zagaya da shi manyan garuruwa irin su Najad da Karbala da ke ƙasar Iraq.
Za mu iya tuna cewa, an kashe jagoran marigayi Ayatullah Ali Khamne'i a watan Fabrairun shekarar 2026 yayin fafatawar yaƙin haɗin gwiwa da ake yi tsakanin Amurika da Isra'ila da kuma ƙasar ta Iran.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post