Gwamnoni Sun Goyi Bayan Ƙirƙirar Sabbin Rundunonin Soji Hudu da Tinubu Ya Amince da Su

Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Nijeriya (NGF) ta bayyana goyon bayanta ga amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙirƙirar sabbin rundunonin Sojin Nijeriya huɗu, tana mai cewa matakin zai ƙara ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar.

A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, ƙungiyar ta ce ƙirƙirar sabbin rundunonin huɗu a lokaci guda ita ce mafi girman faɗaɗa rundunar Sojin Nijeriya da aka taɓa yi a tarihin zamani.

Sanarwar ta ce wannan mataki ya nuna ƙudirin Shugaba Tinubu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma a faɗin ƙasar.

NGF ta kuma yi maraba da amincewar da shugaban ƙasa ya bayar na ɗaukar sabbin jami'an soja 28,000 tare da sayen ƙarin muhimman kayan aikin soja.

Ƙungiyar ta bayyana kwarin gwiwar cewa waɗannan matakai za su ƙara ƙarfafa yaƙi da ta'addanci da kuma ayyukan 'yan bindiga a sassa daban-daban na Nijeriya.

Ta kuma yi alƙawarin ci gaba da yin aiki kafada da kafada da Gwamnatin Tarayya wajen inganta tsaro da kuma sauran muhimman batutuwan ci gaban ƙasa.

Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci 'yan Nijeriya su ci gaba da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen inganta tsaro a dukkan sassan ƙasar.

A baya dai, Shugaba Bola Tinubu ya amince da faɗaɗa rundunar Sojin Nijeriya daga rundunoni takwas zuwa goma sha biyu, tare da ɗaukar sabbin jami'an soja 28,000. Matakin na da nufin rarraba jagorancin ayyukan soja yadda ya kamata, ƙarfafa tsaron iyakoki da kuma inganta martanin rundunar ga sabbin barazanar tsaro a faɗin ƙasar.

A ƙarƙashin sabon tsarin, za a kafa sabbin hedikwatar rundunonin soja a Makurdi, Ilorin, Jalingo da Benin City, yayin da ake sa ran kammala aiwatar da shirin cikin matakai biyu tsakanin watan Satumba da Disambar shekarar 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post