Hamas Ta Sanar da Rushe Gwamnatinta a Gaza domin Tallafa wa Shirin Tsagaita Wuta

Ƙungiyar Hamas ta sanar a ranar Litinin cewa za ta rushe gwamnatinta da ke mulki a Zirin Gaza, matakin da masana suka ce na ƙara matsin lamba ga Isra'ila yayin da ci gaban shirin tsagaita wuta da Amurka ke jagoranta ya tsaya cik.


Shugaban Ofishin Yaɗa Labarai na Gwamnatin Hamas, Ismail al-Thwabta, ya bayyana cewa ƙungiyar a shirye take ta miƙa ragamar mulkin Gaza ga kwamitin ƙwararrun fararen hula na Falasɗinu da aka tanada domin jagorantar yankin bisa yarjejeniyar tsagaita wutar.

Sai dai sanarwar Hamas ba ta yi wani bayani kan batun kwance ɗamarar mayaƙanta ba, wanda ke cikin muhimman sharuɗɗan mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar. Hamas dai ta ci gaba da ƙin amincewa da wannan buƙata.

Ko da yake sanarwar ba ta sauya halin da ake ciki a ƙasa ba, domin Hamas da jami'an tsaronta na ci gaba da iko da sassan Gaza da sojojin Isra'ila ba su mamaye ba, masana sun ce matakin yana mayar da hankali kan abin da ake sa ran Isra'ila za ta yi na cika nata ɓangaren yarjejeniyar.

Shugaban Amurka, Donald Trump, na ci gaba da matsa wa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, lamba domin ci gaba da aiwatar da wasu sassan shirin tsagaita wutar. Daga cikin waɗannan akwai kafa wasu yankuna na gwaji a Gaza, inda Falasɗinawa za su rayu ƙarƙashin jagorancin kwamitin ƙwararrun fararen hula.

Hamas ta kuma yi kira ga masu shiga tsakani da ƙasashen duniya su matsa wa Isra'ila lamba domin ta ba wannan kwamiti damar shiga Gaza.

A cikin wata sanarwa da ya fitar daga Asibitin Shahidan Al-Aqsa da ke Gaza City, Ismail al-Thwabta ya ce:

"Muna kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su hanzarta ɗaukar matakan da za su bai wa Kwamitin Kula da Gudanar da Gaza damar shiga cikin gaggawa tare da fara sauke nauyin da ya rataya a kansa, domin ƙarfafa juriyar al'ummar Falasɗinu da kuma taimaka musu wajen farfaɗowa daga raunukan da suka samu."

A gefe guda kuma, Kwamitin Zaman Lafiya da aka kafa domin sa ido kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ya ce ya lura da sanarwar Hamas, amma zai jira ganin aiyuka maimakon alkawura.

A cikin sanarwar da ya wallafa a shafin X, kwamitin ya sake yin kira ga Hamas da ta kwance ɗamarar mayaƙanta, yana mai jaddada cewa:

"Babban ginshiƙin yarjejeniyar shi ne kasancewar hukuma guda, doka guda da kuma makami guda."

Masanin harkokin Gaza a European Council on Foreign Relations, Muhammad Shehada, ya bayyana cewa sanarwar Hamas wani yunƙuri ne na kai saƙo kai tsaye ga Donald Trump, ba tare da bi ta Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ba.

A cewarsa, Isra'ila na zargin Hamas da ƙin barin mulki, musamman a fannin tsaro. Don haka, Hamas na son nuna cewa a shirye take ta janye gaba ɗaya daga duk wani al'amari da ya shafi tafiyar da gwamnati.

Shehada ya ce Hamas na kallon wannan kwamitin a matsayin hanya ɗaya tilo da za ta bai wa Falasɗinawa damar kafa gwamnati a Gaza wadda ƙasashen duniya za su amince da ita ba tare da wata shakka ba, yana mai bayyana matakin a matsayin dabara mai hikima.

Sai dai ya yi gargadin cewa watakila wannan mataki ya zo ne a makare.

"Ko da Trump ya gamsu da wannan mataki, kuma komai ya tafi yadda aka tsara, Isra'ila ce har yanzu ke da cikakken iko kan duk abin da ke faruwa a Gaza," in ji shi.

Ya ƙara da cewa, "Saboda haka, Isra'ila na iya hana Kwamitin Gudanar da Gaza aiwatar da ayyukansa."

Post a Comment

Previous Post Next Post