Aƙalla Falasɗinawa biyar ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a sassa daban-daban na Zirin Gaza, a ci gaba da rikicin da ke faruwa duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Oktoban bara.
Jami'an lafiya a Gaza sun ce daga cikin waɗanda aka kashe har da yarinya mai shekara tara, bayan harbin da aka yi a wani sansanin masu gudun hijira a yankin Al-Bureij. Haka kuma, wani hari ta sama ya afkawa wani wurin sarrafa ƙarafa a unguwar Sabra da ke birnin Gaza, inda ya kashe wasu mutane da dama tare da jikkata wasu.
Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hare-haren ne kan wuraren da suka bayyana a matsayin cibiyoyin mayaƙan Hamas da wuraren kera makamai, amma ba su tabbatar da dukkan rahotannin da jami'an lafiya na Falasɗinu suka fitar ba.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani wajen samarwa, ana ci gaba da samun hare-hare a Gaza kusan kullum. Hukumomin lafiya na Gaza sun ce sama da Falasdinawa 1,000 sun mutu tun bayan fara aiki da yarjejeniyar, yayin da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Hamas ke ci gaba ba tare da cimma wata babbar nasara ba. Halin jin ƙai a Gaza kuma na ci gaba da taɓarɓarewa, inda miliyoyin mutane ke fama da matsuguni, ƙarancin kayan abinci da magunguna.