INEC ta Tsawaita Wa’adin Mika Sunayen ƴan Takarar Zaben 2027

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ƙara wa'adin da ta bai wa jam'iyyun siyasa na miƙa sunayen 'yan takararsu na zaɓen 2027 kamar yadda kafar Yada labarai ta BBC Hausa ta ruwaito a ranar 12 ga Yuli.INEC ta ce jam'iyyun siyasa yanzu suna da damar miƙa sunayen 'yan takararsu har zuwa tsakar dare na ranar 14 ga Yuli agogon Najeriya.

Hukumar ta bayyana cewa ta yanke wannan shawara ne bayan majalisar tuntuɓa ta jam'iyyun siyasa ta buƙaci hakan sakamakon ƙorafin fuskantar matsaloli wajen saka sunayen ƴantakarar a shafin yanar gizon hukumar.

A cewar INEC, ƙarin wa'adin zai ba bai wa jam'iyyu damar shiga tsarin zaɓe cikin sauƙi tare da tabbatar da bin tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta Najeriya.

Ana sa ran Najeriya za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da majalisun tarayya a watan Janairun 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi za su gudana a watan Fabrairun 2027.

Post a Comment

Previous Post Next Post