Gwamnatin Tarayya Ta Kama Mutane Biyu da Ake Zargi da Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba a Osun

Abuja – Gwamnatin Tarayya ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, a wani samame na haɗin gwiwa da ya kai ga rufe wani sansanin haƙar ma’adinai ba bisa doka ba a Jihar Osun.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Danladi Isa da Musa Kabiru, waɗanda dukkansu matasa ne masu aikin wucin gadi. Hukuma ta ce suna ba masu bincike bayanai masu amfani da za su taimaka wajen gano masu ɗaukar nauyinsu da masu ɗaukar nauyin ayyukan haƙar ma’adinan ba bisa ƙa’ida ba.
An gudanar da samamen ne daga jami’an Ma’aikatar Bunƙasa Albarkatun Ma’adinai ta Tarayya daga jihohin Ogun, Oyo da Osun tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro. An kai farmakin ne sansanonin masu haƙar ma’adinai na gargajiya ba bisa ƙa’ida ba da ke Ileki-Ijesa, a kan hanyar Ile-Ife zuwa Ilesa.
A cikin wata sanarwa da Mataimakiya ta Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Ministan Bunƙasa Albarkatun Ma’adinai, Lara Owoeye-Wise, ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri game da ayyukan masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da ke gudana a yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an rundunar musamman ta ma’adinai sun mamaye wurin bayan samun bayanan sirri. Da zarar masu haƙar ma’adinan suka hangi tawagar jami’an tsaro, da dama daga cikinsu sun tsere zuwa cikin daji. Sai dai jami’an sun yi nasarar cafke mutane biyu tare da ƙwace kayayyaki da na’urorin da ake amfani da su wajen gudanar da haramtacciyar haƙar ma’adinai.
Baya ga haka, jami’an sun rusa manyan sansanonin ayyukan da masu haƙar ma’adinan suka kafa tare da rufe wurin bisa tanade-tanaden Dokar Ma’adinai da Haƙar Ma’adinai ta Najeriya.
Kayayyakin da aka ƙwace sun haɗa da babura guda biyu, injinan famfo, janaretocin Lister, na’urorin wanke ma’adinai, manyan bututun roba, tabarmomin tace zinariya, adduna da sauran kayan aikin haƙar ma’adinai da ake zargin an yi amfani da su wajen ayyukan ba bisa ƙa’ida ba.
Da yake jawabi yayin samamen, Jami’in Ma’adinai na shiyyar Kudu maso Yamma, Ajibade Ganiyu, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce farmakin wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da bin Dokar Ma’adinai da Haƙar Ma’adinai ta Najeriya, kare muhalli, kare rayuka da kuma hana wawure albarkatun ma’adinan ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.
Ya jaddada cewa ma’aikatar za ta ci gaba da gudanar da sintiri da samame a jihohin Kudu maso Yamma da sauran sassan ƙasar domin murƙushe ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba tare da dawo da doka da oda a fannin.
Shi ma Jami’in Ma’adinai na Jihar Osun, Wasiu Adeboye, ya ce wannan samame ya zama gargaɗi ga duk masu hannu a ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa doka ba cewa gwamnati ba za ta ƙara lamunta da su ba.
Ya ce, “Wannan samame ya aika da saƙo a sarari cewa ba za a ƙara yarda da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a ko’ina cikin ƙasar nan. Masu ɗaukar nauyi, masu ba da kuɗi da masu aikata irin waɗannan laifuka su sani cewa za su ci gaba da fuskantar hukunci bisa tanadin doka. Za mu ci gaba da irin waɗannan ayyuka har sai an shawo kan wannan matsala.”
A nasa ɓangaren, Ministan Bunƙasa Albarkatun Ma’adinai, Dele Alake, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta mayar da gyaran fannin ma’adinai da kawar da ayyukan ba bisa ƙa’ida ba a matsayin muhimmin abin da ta sa a gaba. Ya ce ana cimma hakan ne ta hanyar ƙarfafa aiwatar da doka, gyaran manufofi, tattara bayanan sirri da kuma haɗa kan al’ummomin yankunan da ake haƙar ma’adinai.
A cewarsa, kafa rundunar Mining Marshals ta ƙara wa gwamnati ƙarfi wajen yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, inda aka kama fiye da mutum 300 tare da gurfanar da sama da mutum 150 a gaban kotu, ciki har da wasu baƙin haure, yayin da aka kuma rufe wuraren haƙar ma’adinai ba bisa doka ba da dama a faɗin ƙasar.
Ministan ya bayyana cewa waɗannan samame da ake ci gaba da gudanarwa a faɗin ƙasar wani ɓangare ne na dabarun tabbatar da cewa albarkatun ma’adinan Najeriya suna amfanar ƙasa ta hanyar haƙar ma’adinai cikin doka, gaskiya da ɗaukar alhakin kare muhalli.
Ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa da mazauna yankunan da ake haƙar ma’adinai da su mara wa gwamnati baya ta hanyar ƙin ba masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba mafaka, tare da bai wa jami’an tsaro da ma’aikatar sahihan bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙi da wannan matsala.

Post a Comment

Previous Post Next Post