Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano ta sanar da fara rajistar aikin Hajjin shekarar 2027 tare da kayyade Naira miliyan 8 a matsayin kuɗin ajiya na farko ga masu niyyar zuwa aikin Hajji.
Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar hukumar ranar Lahadi.
Ya ce an kayyade adadin kuɗin ne bayan tuntuba da nazari mai zurfi, yana mai ƙarawa da cewa an tanadi tsarin biyan kuɗi na gaskiya da tsari.
Matawalle ya bayyana cewa dukkan kuɗaɗen za a biya ne ta hanyar bank draft, sannan a miƙa su ga jami'an cibiyoyin Hajji na ƙananan hukumomi a faɗin jihar.
Ya kuma gargaɗi masu niyyar zuwa Hajji da su bi hanyoyin da gwamnatin jihar Kano ta amince da su kawai, tare da guje wa mu'amala da mutanen da ba su da izini.
A cewarsa, za a fara sayar da kujerun Hajji da karɓar kuɗin rajista daga 12 ga watan Yuli, 2026, kuma za a rufe rajistar a 26 ga watan Satumba, 2026.
Darakta Janar ɗin ya buƙaci masu niyyar zuwa Hajji su gaggauta yin rajista da biyan kuɗi domin kauce wa cunkoso a ƙarshen wa'adi da kuma bai wa hukumar damar shirya aikin Hajjin yadda ya kamata.
Ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Kano bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar da alhazai, tare da yaba wa malamai, masu ruwa da tsaki da al'ummar jihar Kano kan haɗin kai da amincewar da suke bai wa hukumar.
A ƙarshe, Matawalle ya yi addu'ar Allah Ya karɓi niyyar duk masu shirin zuwa Hajji, Ya ba su ikon gudanar da Hajji karɓaɓɓe, tare da dawo da su gida lafiya.
