Kotun Ukraine Ta Tsare Wadanda Ake Zargi da Kashe Babbar Wadda Ake Zargi Da Harin Bam a Monaco

 Wata kotu a Ukraine ta ba da umarnin tsare wasu maza biyu ba tare da beli ba, bayan ana zarginsu da kashe Anastasiia Berezovska, wata 'yar Ukraine da ake nema ruwa a jallo kan zargin kai harin bam a ƙasar Monaco.

Anastasiia Berezovska

An zargi Berezovska da dasa bam a ranar 29 ga Yuni wanda ya raunata ɗan kasuwar da aka haifa a Ukraine, Vadym Yermolaiev, tare da abokiyar zamansa da ɗansa. Bayan harin, ta tsere ta wasu ƙasashen Turai kafin ta koma Ukraine, inda daga bisani aka same ta a kashe da harbin bindiga kusa da Kyiv.

Masu gabatar da ƙara sun ce waɗanda ake zargin sun haɗa da wani jami'in Hukumar Leken Asirin Sojin Ukraine (HUR) da kuma wani tsohon jami'in tsaro. Daya daga cikinsu ya fara amsa cewa yana da hannu a kisan, amma daga baya ya janye furucin nasa, yana mai zargin ɗayan mutumin ne ya aikata kisan, yayin da shi ya taimaka ne saboda tsoro.

Masu bincike sun ce sun gano harsasai a wurin da aka kashe matar, tare da wasu shaidu da suka haɗa da wani ɗaki da ake zargin an yi amfani da shi wajen azabtar da mutane. Lauyoyin waɗanda ake zargin sun musanta cewa abokan huldarsu ne suka kashe matar, suna masu cewa binciken ya kamata ya ci gaba domin gano gaskiyar lamarin. 

Lamarin ya jawo hankalin hukumomin Monaco, Ukraine da Faransa, yayin da ake ci gaba da bincike kan ko akwai alaƙa tsakanin harin bam da kuma kisan matar da ake zargi.

Post a Comment

Previous Post Next Post