Tsohuwar Firaminista Hasina Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa Ta Shirya Komawa Bangladesh a Disamba

 Tsohuwar Firaministar Bangladesh, Sheikh Hasina, ta bayyana cewa tana shirin komawa ƙasarta a watan Disamba, duk da cewa tana fuskantar hukuncin kisa da wata kotu ta yanke mata ba tare da ta halarta ba. Hasina, wadda ke gudun hijira a Indiya, ta ce za ta koma Bangladesh tare da wasu manyan shuwagabannin jam’iyyarta ta Awami League domin su miƙa kansu ga kotu.

Sheikh Hasina

Hasina ta ce a shirye take ta fuskanci duk wani sakamako da zai biyo bayan dawowarta, ciki har da yiwuwar kama ta ko kuma mutuwa. Ta bayyana cewa tana son ta fuskanci shari’a a ƙasarta, inda ta ce ya kamata jama’ar Bangladesh su yanke hukunci kan ayyukan gwamnatinta.

Tsohuwar shugabar ta tsere daga Bangladesh zuwa Indiya a shekarar 2024 bayan zanga-zangar da ɗalibai suka jagoranta ta kawo ƙarshen mulkinta na kusan shekaru 20. Daga baya, wata kotun laifukan ƙasa da ƙasa ta Bangladesh ta yanke mata hukuncin kisa bisa zarge-zargen laifukan cin zarafin bil’adama da suka shafi murƙushe zanga-zangar, zargin da ta musanta.

Hasina ta kuma soki haramta ayyukan jam’iyyarta ta Awami League, inda ta ce tana ƙoƙarin sake tsara jam’iyyar ta hanyar tarurrukan yanar gizo da shugabanninta. Dawowarta na iya haifar da sabon tashin hankali na siyasa a Bangladesh, yayin da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin bangarorin siyasa daban-daban.

Jami’an gwamnatin Bangladesh da na Indiya ba su fitar da cikakken martani kan shirin dawowar nata ba, duk da cewa Indiya a baya ta ce tana nazarin buƙatar Bangladesh kan yiwuwar mika Hasina ga hukumomin ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post