Likitocin Yara Sun Gargaɗi Iyaye Kan Yi Wa Jarirai Wanka da Ruwan Sanyi A Lokacin Damina

Likitocin ƙwararru kan lafiyar yara sun gargaɗi iyaye da masu kula da yara da su guji yi wa jarirai da ƙananan yara wanka da ruwan sanyi, musamman a lokacin damina, suna mai cewa hakan na iya jefa su cikin matsalar sanyin jiki mai tsanani (hypothermia) tare da ƙara haɗarin kamuwa da cututtuka.

Sun bayyana cewa kiyaye jarirai cikin yanayi mai ɗumi, musamman lokacin yi musu wanka, na daga cikin matakan kariya mafi sauƙi amma masu matuƙar muhimmanci wajen hana kamuwa da cututtukan da za a iya kauce musu a lokacin sanyi.

Likitocin sun yi karin haske cewa ruwan sanyi ba shi ne ke haddasa ciwon huhu (pneumonia) kai tsaye ba. Sai dai suna iya rage ƙarfin garkuwar jikin yaro ko kuma su tayar da matsalolin lafiya da yake fama da su tun da farko, musamman ga masu cutar asma da sikila.

Wannan gargaɗi na zuwa ne yayin da Najeriya ke fuskantar lokacin da damina ta kai ƙololuwa, wanda ke tattare da raguwar yanayin zafi, musamman da sassafe da kuma bayan ruwan sama na dare.

Bayanan Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) sun nuna cewa damina, wadda kan fara daga ƙarshen watan Fabrairu, kan kai ƙololuwarta tsakanin watan Yuli da Agusta, inda ake samun yawan ruwan sama da sanyin yanayi a sassa da dama na ƙasar.

A wannan lokaci, yanayin zafin ruwa kan ragu, lamarin da ke ƙara haddasa damuwa game da illar da sanyin ruwa zai iya yi wa jarirai.

Hypothermia wata matsala ce da ke faruwa idan zafin jikin mutum ya ragu zuwa matakin haɗari, saboda jiki na rasa zafi fiye da yadda yake samar da shi. Jarirai sun fi fuskantar wannan matsala saboda jikinsu bai gama bunƙasa wajen daidaita yanayin zafi ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), a cikin shawarwarinta kan kula da jarirai da kare su daga sanyi, ta jaddada muhimmancin tabbatar da cewa jarirai suna cikin ɗumi, tana mai cewa suna da saurin rasa zafin jikinsu.

Haka kuma, Ƙungiyar Likitocin Yara ta Amurka (American Academy of Pediatrics), ta hanyar shirin HealthyChildren, ta ba da shawarar amfani da ruwan ɗumi da kuma yin wanka a muhalli mai ɗumi yayin kula da jarirai.

Da yake zantawa da PUNCH Healthwise kan batun, Shugaban Sashen Kula da Lafiyar Yara na Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, Dr. Abdurrazzaq Alege, ya bayyana cewa jarirai sun fi fuskantar haɗarin sanyi.

Ya ce, "Jarirai suna rasa zafin jikinsu cikin sauri fiye da manya saboda jikinsu bai gama bunƙasa yadda zai iya daidaita yanayin zafi ba. Idan aka yi musu wanka da ruwan sanyi a lokacin da yanayi yake da sanyi, suna iya shiga matsalar hypothermia cikin sauƙi."

Dr. Alege ya kuma ƙaryata ra'ayin da ya yadu cewa sanyi ne ke haddasa ciwon huhu kai tsaye.

Ya ce, "Ba yanayin sanyi ko ruwan sanyi ne ke haddasa ciwon huhu ba. Ciwon huhu ƙwayoyin cuta ne, ko na ƙwayoyin bacteria ko kuma virus, ke haddasa shi. Abin da sanyi ke yi shi ne rage ƙarfin garkuwar jiki, wanda hakan ke sa yara su fi saurin kamuwa da irin waɗannan cututtuka."

A cewarsa, ba duk yaron da ya shiga sanyi ba ne zai kamu da rashin lafiya, amma yaran da ke da wasu matsalolin lafiya tun farko sun fi kasancewa cikin haɗari, domin sanyi na iya tayar ko tsananta matsalolin da suke fama da su.

Ya ce idan ƙarfin garkuwar jiki ya ragu, ƙwayoyin cuta kan samu damar kai hari, wanda hakan kan haifar da tari, mura da wahalar numfashi.

Dr. Alege ya shawarci iyaye su rika lura da yaransu idan suna zargin sun shiga sanyi, yana mai cewa hanya mafi inganci ita ce amfani da na'urar auna zafin jiki ta dijital (digital thermometer), musamman ta hanyar sanya ta a hammata. Ya kuma ba da shawarar cewa ya dace kowanne gida ya mallaki irin wannan na'ura.

Dangane da yadda ya kamata a yi wa jarirai wanka a lokacin sanyi, ya ce, "A yi amfani da ruwan ɗumi, a tabbatar ɗakin wankan yana da ɗumi, sannan a goge jariri tare da rufe shi da tufafi masu ɗumi nan take bayan an gama wanka."

Ya kuma yi watsi da ikirarin cewa yi wa jarirai wanka da ruwan sanyi yana ƙarfafa jikinsu, yana mai cewa babu wata hujjar kimiyya da ta tabbatar da hakan.

Shi ma ƙwararren likitan yara kuma mai fafutukar wayar da kan jama'a kan lafiyar yara, Dr. Ayodele Renner, ya jaddada muhimmancin kiyaye jarirai cikin ɗumi.

Ya ce, "Ga jarirai sabbin haihuwa, tsarin daidaita zafin jiki bai gama bunƙasa ba. Duk wani sauyin sanyi na gaggawa, ciki har da yi musu wanka da ruwan sanyi, na iya jefa su cikin matsala cikin ƙanƙanin lokaci."

Ya ƙara da cewa idan zafin jikin yaro ya ragu, jikinsa zai fara kashe kuzari mai yawa wajen samar da zafi, wanda hakan kan shafi shayarwa, girma da lafiyarsa gaba ɗaya.

Dr. Renner ya sake fayyace cewa ciwon huhu ƙwayoyin cuta ne ke haddasa shi, yayin da sanyi kawai ke rage ƙarfin garkuwar jiki, wanda hakan ke bai wa ƙwayoyin cuta damar haddasa rashin lafiya.

Ya kuma yi gargadin cewa yawaita fallasa yara ga yanayin sanyi na iya sa su riƙa kamuwa da cututtuka akai-akai.

A ƙarshe, ya shawarci iyaye da su tabbatar sun gwada zafin ruwan kafin su yi wa jariri wanka, su takaita lokacin wankan, sannan su naɗe ko su rufe jaririn da tawul ko tufafi masu ɗumi nan take bayan sun gama.

Post a Comment

Previous Post Next Post