Yayin da ake ci gaba da samun ruwan sama mai ƙarfi kamar yadda Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashe, masana harkokin lafiya sun yi gargaɗin cewa ambaliyar ruwan da ta mamaye Jihar Legas na iya haifar da barkewar cututtuka irin su kwalara, maleriya da taifod, yayin da jihar ke fama da asarar dukiya, koma bayan tattalin arziki da kuma ƙarin damuwa kan matakan magance ambaliyar ruwa.Ruwan saman da aka fara samu tun ranar Lahadi ya mamaye tituna da gidaje, ya jefa matafiya da masu ababen hawa cikin wahala, tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci da sauran ayyukan yau da kullum, yayin da al'ummomi da dama a faɗin jihar ke ci gaba da tantance irin asarar da suka yi sakamakon cikar magudanan ruwa.
Wani ƙwararren masani kan lafiyar jama'a, Dakta Godswill Iboma, ya yi gargaɗin cewa ambaliyar ruwa da ta mamaye Legas da sauran sassan ƙasar na iya haddasa barkewar cututtukan kwalara, taifod, maleriya da sauran cututtukan da ruwa ko sauro ke yaɗawa. Ya buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa su ƙara kula da tsaftar abinci, ruwan sha da kuma muhallansu.
Da yake zantawa da jaridar The Guardian, Iboma ya bayyana cewa gurɓataccen ruwan ambaliya da kuma ruwan da ke tsayawa bayan ruwan sama suna samar da yanayi mai sauƙaƙa yaɗuwar cututtuka. Ya ce ambaliya na ƙara haɗarin kamuwa da gudawa, kwalara da taifod saboda tana gurɓata hanyoyin samun ruwan sha, yayin da ruwan da ya tsaya ke zama mafakar haihuwar sauro, abin da ke ƙara haɗarin barkewar cutar maleriya.
Iboma ya danganta tsanantar ambaliyar ruwa a yankuna da dama da lalacewar muhalli, musamman zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba, wanda ke toshe magudanan ruwa tare da ƙara muni ga matsalar ambaliya.
Ya shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar ambaliya da su tafasa ruwan sha idan ba a tabbatar da tsabtarsa ba, su rika rufe abinci yadda ya kamata domin kauce wa gurɓatawa, sannan su rika amfani da gidajen sauro masu ɗauke da maganin kashe sauro ko kuma magungunan korar sauro domin rage haɗarin kamuwa da maleriya.
Haka kuma, masanin ya yi kira ga jama'a da su kasance cikin shiri da taka-tsantsan, yana mai gargaɗin cewa ambaliyar ruwa na iya tilasta macizai da sauran dabbobi masu haɗari barin mazaunansu su shiga cikin unguwannin da mutane ke zaune.