"Rancen Karatun NELFUND Ya Hana Ni Barin Jami'a" — Dalibin UNILAG

Wani ɗalibin mataki na uku (300 Level) a Jami'ar Legas (UNILAG), Migwe Obinna Nicholas, ya bayyana yadda Asusun Tallafin Rancen Karatun Najeriya (NELFUND) ya ceci karatunsa daga tsayawa, yana mai cewa shi ne kaɗai a cikin iyalinsa da ya samu damar shiga jami'a.

Nicholas, wanda ke karantar Fannin Wasan Kwaikwayo da Nazarin Fina-finai a UNILAG, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tsohon ɗan shirin Big Brother Naija, DeeOne, wadda aka wallafa a shafinsa na Instagram ranar Litinin.

Ɗalibin ya ce a halin yanzu yana zaune ne a cocin da yake ibada saboda ba shi da masaukin kansa, bayan ya bar gidan 'yar uwarsa sakamakon saɓani da mijinta.

Ya ce, "Ni ne kaɗai a cikin iyalina da na kai jami'a. A halin yanzu ina amfani da rancen karatu wajen biyan kuɗin karatuna. Ina kwana a cocin da nake ibada domin ba ni da gida na kaina."

Nicholas ya bayyana cewa ya taso ne a cikin iyali mai ƙaramin ƙarfi, inda yana ɗan shekara takwas ya bar Jihar Ebonyi zuwa Legas domin zama tare da 'yar uwarsa.

A cewarsa, duk da irin goyon bayan da 'yar uwarsa ta ba shi tsawon shekaru, sai ya bar gidanta bayan samun gurbin karatu a UNILAG, saboda mijinta yana son ya daina karatu ya shiga kasuwancinsa na sayar da kayan haɗi (accessories).

Ya ce, "Na fito daga iyali mai talauci kuma mai matsaloli. Na kasance tare da 'yar uwata tun ina ɗan shekara takwas. Amma bayan na samu gurbin karatu a Jami'ar Legas, mijinta ya ce in bar gidansu. Yana so ne in shiga kasuwancinsa na sayar da kayan haɗi, amma burina shi ne in yi karatu sannan in zama mawaƙi."

Nicholas, wanda ke amfani da sunan fasaha BMX Royce, ya ce da farko ya sha wahala sakamakon ƙarin kuɗin makaranta da aka yi.

Ya bayyana cewa har ya fara tunanin barin jami'a kafin ya nemi rancen karatu na Gwamnatin Tarayya.

A cewarsa, "Na kusa daina karatu, amma na nemi rancen saboda ban so in hakura ba. Da ba a ba ni rancen ba, Allah kaɗai ya san abin da zai faru da ni. Gaskiya na kusa barin jami'a kusan zangon karatu biyu da suka gabata."

Ɗalibin ya ƙara da cewa NELFUND na biyan masa kuɗin makaranta a halin yanzu, sai dai kuɗin tallafin kula da kai na wata-wata ba sa zuwa a kai a kai.

Ya bayyana cewa masu cin gajiyar shirin na iya neman a biya musu kuɗin makaranta tare da samun tallafin kula da kai na naira 20,000 a kowane wata.

Post a Comment

Previous Post Next Post