Rangwamen Harajin Shigo da Kaya Ya Kai Naira Tiriliyan 34 a 2025 – Kwastam

Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Bashir Adeniyi, ya bayyana a ranar Litinin cewa darajar takardun amincewar rangwamen harajin shigo da kaya da kayan aiki (Import Duty Exemption Certificate – IDEC) da Gwamnatin Tarayya ta bayar kan wasu kayayyaki da na'urorin da aka shigo da su daga ƙasashen waje ta kai Naira tiriliyan 34 a shekarar 2025.
Adeniyi ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan rangwamai na manufofin gwamnati sun yi matuƙar rage ƙarfin Hukumar Kwastam wajen tara kuɗaɗen shiga.
Ya bayyana hakan ne yayin zaman bincike da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kuɗi ya gudanar da hukumomin gwamnati masu tara kuɗaɗen shiga a Abuja.
A wannan zama ne kuma kwamitin ya yi barazanar ɗaukar matakin ladabtarwa kan shugabannin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), Hukumar Bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Masana'antu (SMEDAN), Asusun Horar da Ma'aikata (ITF), Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jabi (FMC Jabi), da wasu hukumomi saboda rashin amsa gayyatar da aka yi musu.
Da yake jawabi a gaban sanatoci, Adeniyi ya ce manufofin kasafin kuɗi na gwamnati kan yi tasiri kai tsaye ga yadda Hukumar Kwastam ke tara kuɗaɗen shiga, walau ta fuskar ƙaruwa ko raguwa.
Ya ce duk da cewa Hukumar Kwastam na daga cikin manyan hukumomin da ke samar wa gwamnati kuɗaɗen shiga, da ta samu damar tara kuɗi fiye da yadda take yi da ba don rangwamen haraji da sauran tsare-tsaren gwamnati ba.
A cewarsa, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka fi shafar kuɗaɗen shiga na hukumar shi ne tsarin Takardar Rangwamen Harajin Shigo da Kaya (IDEC), wanda aka fara aiwatarwa tun a watan Maris na shekarar 2020.
Ya ce, "Darajar takardun IDEC da aka amince da su ta kai kusan Naira tiriliyan 34 a shekarar 2025, inda kashi 60 cikin 100 daga cikinsu suka shafi sayen kayan aikin soja da gwamnati ta yi, waɗanda aka ba su rangwamen haraji saboda ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta."
Ya ƙara da cewa sauran kayayyakin da suka ci gajiyar rangwamen sun haɗa da kayan aikin iskar gas ta CNG, motocin lantarki da masu amfani da haɗaɗɗen makamashi (hybrid), kayan aikin asibitoci da magunguna, injinan masana'antu da kayan sarrafawa, da kuma shirye-shiryen gwamnati na shigo da kayan abinci.
Sai dai Adeniyi ya jaddada cewa bai kamata a rika auna nasarar manufofin kasafin kuɗi da yawan kuɗaɗen shiga kaɗai ba, domin rangwamen haraji na taimakawa wajen cimma wasu manyan manufofin tattalin arziki da walwalar al'umma.
Duk da haka, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa tsarin sa ido domin tabbatar da cewa waɗanda suka amfana da rangwamen sun cika manufofin da aka sa gaba, ciki har da rage farashin kayayyaki, ƙara yawan samar da kayayyaki a masana'antu da kuma inganta samun kayan aikin lafiya.
Tun da farko a jawabinsa, Adeniyi ya sanar da kwamitin cewa Hukumar Kwastam ta tara Naira tiriliyan 4.5 zuwa ranar 30 ga Yunin 2026, daga cikin burin tara Naira tiriliyan 11.04 da aka sanya mata na shekarar 2026. Hakan na nufin akwai kusan Naira tiriliyan 7 da har ake sa ran za a tara kafin ƙarshen shekarar kuɗi.
Zaman ya kuma bayyana saɓani kan zargin cewa wasu hukumomin gwamnati ba su mayar da rarar kuɗaɗen gudanar da ayyukansu cikin Asusun Haɗaɗɗen Kuɗaɗen Shiga na Tarayya (Consolidated Revenue Fund).
Da yake wakiltar Hukumar Fiscal Responsibility Commission (FRC), Mataimakin Daraktan Sa Ido da Tantancewa, Bello Gulmare, ya zargi Hukumar Kwastam da bin gwamnatin tarayya bashin Naira biliyan 8.9, sakamakon rashin mayar da rarar kuɗaɗen gudanar da ayyukanta tun daga shekarar 2019.
Sai dai jami'an Hukumar Kwastam sun yi watsi da wannan zargi.
Haka kuma, Hukumar FRC ta zargi Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Ƙasa (CAC) da bin gwamnati Naira biliyan 13.9 na rarar kuɗaɗen gudanar da ayyuka da ba a mayar ba tsakanin shekarun 2023 zuwa 2025.
Da yake mayar da martani, Babban Magatakardan CAC, Hussaini Ishaq Magaji, ya ce hukumar na ci gaba da biyan waɗannan kuɗaɗe a matakai.
Bayan sauraron bayanan, Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kuɗi ya umarci CAC da Hukumar FRC tare da sakatariyar kwamitin su daidaita bayanansu domin gano ainihin adadin bashin da ya rage.
Shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa mai wakiltar mazabar Niger ta Gabas, ya ce dole ne a kammala aikin daidaita bayanan cikin makonni biyu kafin wani sabon zama da za a yi da hukumar.
Ya kuma yi gargaɗin cewa shugabannin hukumomin da suka haɗa da NCAA, ITF, SMEDAN, FMC Jabi da sauran waɗanda ba su halarci zaman ba, su tabbatar sun halarci zama na gaba, in ba haka ba za a ɗauki tsauraran matakan ladabtarwa a kansu bisa tanadin dokokin Majalisar Dattawa.
A cikin 'yan watannin nan, Majalisar Dattawa ta ƙara ƙaimi wajen sa ido kan hukumomin gwamnati masu tara kuɗaɗen shiga domin ƙara yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati, tabbatar da bin Dokar Fiscal Responsibility Act, da kuma tabbatar da cewa ana mayar da rarar kuɗaɗen gudanar da ayyuka cikin Asusun Haɗaɗɗen Kuɗaɗen Shiga na Tarayya.
Haka kuma, Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kuɗi na ci gaba da nazarin tasirin rangwamen haraji da keɓance harajin shigo da kaya kan kuɗaɗen shiga na ƙasa, a daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da ba na man fetur ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post