Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gadon marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya ginu kan gaskiya, ɗa’a da hidima ga ƙasa ba tare da son kai ba, zai ci gaba da zaburar da al’ummomin Najeriya na yanzu da na gaba.
Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilta a bikin tunawa da cikar shekara guda da rasuwar Buhari da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, ya bayyana marigayin a matsayin ɗan kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen ci gaban Najeriya. Ya ce kyawawan ɗabi’unsa na gaskiya, ɗa’a da hidima za su ci gaba da zama abin koyi ga al’umma.
Shugaban ya ce Buhari ya ci gaba da kasancewa cikin girmamawar ƴan Najeriya ko bayan ya sauka daga mulki, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da rungumar kyawawan halayen da ya rayu da su.
Tinubu ya ce, “Mun hallara a nan yau, shekara guda bayan rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, GCFR, domin rayuwar da ya yi ba irin wadda wannan ƙasa za ta taɓa mantawa da ita ba ce. Ya riga ya zama wani ɓangare na tarihin Najeriya, kuma irin waɗannan mutane ana ci gaba da tuna su ko bayan sun riga mu gidan gaskiya.
“Ba wai saboda wata al’ada muka taru ba, sai dai domin mu sake waiwayar irin gudummawar da Buhari ya bayar ga ƙasa; a matsayin aboki, shugaba, uba, miji da kuma ɗan ƙasa nagari.
“Ni da Buhari mun yi tafiya tare a fagen siyasa da gina ƙasa. Mun fuskanci lokutan ƙalubale da na fata tare. Burinmu shi ne ganin Najeriya ta zama ƙasa mai ci gaba, haɗin kai, zaman lafiya da wadata, inda babu wani ɗan ƙasa da za a bari a baya.
“Ya sadaukar da duk abin da yake da shi domin hidimar ƙasarsa ba tare da wata shakka ba. Ya yi aiki da jarumtaka, cikakken imani da kishin ƙasa. Tun daga lokacin da ya jagoranci ƙasa a matsayin soja har zuwa lokacin da ya zama shugaban ƙasa ta hanyar dimokuraɗiyya, Buhari ya kasance abin koyi wajen kawo sauyi da gina ƙasa.”
Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan tsirarun shugabannin Najeriya da suka jagoranci ƙasar a matsayi biyu daban; na shugaban mulkin soja da kuma shugaban ƙasa da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya.
Ya ƙara da cewa amincewa da ƙaunar da ƴan Najeriya suke yi wa Buhari sun ci gaba har bayan ya sauka daga mulki, yana mai cewa gadonsa ya ta’allaka ne kan mutunci, nagarta da hidima, ba wai neman yabo ba.
Shugaban ya kuma jajanta wa iyalan marigayin, musamman tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, da sauran ‘ya’yansa, yana mai tabbatar musu cewa gwamnati da al’ummar Najeriya za su ci gaba da kasancewa tare da su, tare da addu’ar Allah Ya ba su haƙuri da juriya.
Ya ce nauyin da ke kan abokansa, almajiransa da abokan aikinsa shi ne su ci gaba da ɗaukar darussan gaskiya, sauƙin kai da ɗa’ar da ya bari.
A nasa jawabin, tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon, ya ce dangantakarsa da Buhari ta samo asali tun lokacin da suke aikin soja tare, inda ya bayyana shi a matsayin jarumin soja kuma shugaba mai kishin haɗin kan Najeriya.
Gowon ya ce Buhari ya sha yin takarar shugaban ƙasa ba tare da nasara ba, har sai da ya haɗa kai da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu suka kafa ƙawancen siyasa wanda ya kai shi ga lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2015.
Ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Buhari, sannan daga bisani Buhari ma ya mara wa Tinubu baya domin ya gaje shi a shugabancin ƙasar.
Gowon ya kuma tuna yadda tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya amince da sakamakon zaɓen 2015 kafin a kammala bayyana sakamakon gaba ɗaya, yana mai cewa Buhari ya nuna ƙwarewar shugabanci ta hanyar karɓar wannan mataki cikin mutunci, abin da ya taimaka wajen kauce wa rikicin zaɓe a Najeriya.
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, wanda Mataimakinsa Faruk Lawal Jobe ya wakilta, ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya, ɗa’a da kishin haɗin kan Najeriya.
Ya ce gudummawar Buhari ba ta tsaya ga siyasa kaɗai ba, domin ta haɗa da bunƙasa ababen more rayuwa, noma, tsaro da ci gaban zamantakewa. Ya ƙara da cewa rayuwarsa mai sauƙi da sadaukarwa ga hidimar jama’a sun sa ya samu girmamawa a faɗin ƙasar nan.
Tun da farko, Shugaban Kwamitin Shirya Taron Tunawa da Rasuwar Buhari kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce taron wata dama ce ta tuna rayuwar hidima da sadaukarwar Buhari ga Najeriya.
Ya ce rasuwar Buhari ta jefa Najeriya, Afirka da sauran sassan duniya cikin jimami, yayin da jana’izarsa a Daura ta haɗa shugabanni, manyan jami’an gwamnati, sarakuna, malamai da dubban ‘yan Najeriya daga sassa daban-daban, abin da ya nuna irin ƙimar da marigayin yake da ita a zukatan jama’a.
A nata jawabin, ɗiyar marigayin, Safina Buhari, ta gode wa duk waɗanda suka halarci taron tunawa da mahaifinta, tana mai cewa rayuwarsa ta ginu ne kan imani, gaskiya, ɗa’a, tawali’u, kishin ƙasa da hidimar jama’a.
Ta bayyana cewa an ba da kuɗaɗen da aka samu daga littafin “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari” ga Jami’ar Al-Qalam da ke Katsina domin gina Cibiyar Nazarin Kimiyyar Kwamfuta, a matsayin cika burin marigayin na tallafa wa ilimi da bunƙasa rayuwar al’umma.
Ta ce cibiyar, wadda aka ƙaddamar a ranar 5 ga Yuli, za ta ƙunshi dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje na kwamfuta, ofisoshi da sauran kayayyakin more ilimi.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Hajiya Aisha Buhari, Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Ogun Dapo Abiodun, Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari, tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika, Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi Atiku Bagudu, tsohon Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed, da sauran manyan baƙi.