TARIHIN HADUWAR SIFANIYA DA AJANTINA A GASAR CIN KOFIN DUNIYA

TARIHIN HADUWAR SIFANIYA DA AJANTINA A GASAR CIN KOFIN DUNIYA

Duk da cewa Sifaniya (Spain) da Ajantina (Argentina) fitattu kuma sanannun ƙasashe ne da suka daɗe suna taka rawa a gasar cin kofin duniya, amma dai ba su taɓa haɗuwa a gasar cin kofin duniya ba sai dai ɗaya, wanda aka yi shi a jihar Birmingham da ke ƙasar Ingila shekarar da Ingilar ta karɓi baƙuncin wasan.

A cewar tarihin FIFA, ƙungiyoyin biyu sun taɓa hadyuwa sau ɗaya tak a gasar cin kofin duniya. Wannan ya faru ne a ranar 13 ga Yuli, 1966, a filin Villa Park da ke Birmingham, Ingila.

A Wasan da aka fafata a shekarar 1966 Argentina ce ta yi nasara da 2-1 a wasannin zagayen rukuni na Kofin Duniya na 1966. Dukkanin Ƙwallaye ukun an ci su ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci. Luis Artime ne ya zura ƙwallaye biyu ga Argentina a mintuna 65 da 77, yayin da Pirri ya ci wa Spain a minti na 71.

Sakamakon ya ba Argentina damar ci gaba da fafatawa a rukunin, sai dai daga baya Ingila ta fitar da su a wasan daf da na kusa da na ƙarshe (Quarter Final). Ita kuma Spain an fitar da ita tun a matakin rukuni.

Bayan wannan wasan na 1966, shekaru 60 ke nan, Spain da Argentina ba su sake haɗuwa a Kofin Duniya ba, sai ranar Lahadi 19 ga watan Yuli, 2026. Wasan da za a fafata a filin New York New Jersey Stadium a Amurka, kuma shi ne wasan karshe na gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da zakarun Turai na yanzu, Spain, da zakarun Kudancin Amurka, Argentina, za su haɗu a wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya.


Duk da ƙarancin haɗuwarsu a gasar cin Kofin Duniya, Spain da Argentina sun buga wasanni 14 gabaɗaya tun 1952. Kowane ɓangare ya yi nasara sau 6, yayin da wasa 2 suka tashi canjaras.

Wasan ƙarshe da suka buga kafin 2026 shi ne na sada zumunci a Maris 2018, inda Spain ta doke Argentina da ci 6-1 a Madrid.


Spain: ta taɓa lashe Kofin Duniya sau 1 a shekarar 2010. Yayin da Argentina kuma ta lashe shi sau 3, a shekarun 1978, 1986 da kuma 2022.

Post a Comment

Previous Post Next Post