Shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa, ya sanar da yin manyan sauye-sauye a shuwagabancin hukumomin tsaro da leƙen asiri na ƙasar, inda ya naɗa sabbin jami'ai a muhimman muƙamai domin ƙarfafa hukumomin tsaro da inganta gudanar da ayyukansu.
Sauye-sauyen sun shafi manyan hukumomin tsaro da leken asiri, inda sabbin shugabanni suka maye gurbin wasu jami'an da suka daɗe suna riƙe da waɗannan mukamai.
A cewar gwamnatin Syria, an yi wannan sauyi ne domin inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, ƙara ingancin ayyukansu, da kuma fuskantar sabbin ƙalubalen tsaro da ƙasar ke ciki.
Matakin ya zo ne yayin da Syria ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a wasu yankuna, tare da ƙoƙarin farfaɗo da ƙasar bayan shekaru na rikici. Masana na ganin cewa sauye-sauyen na iya kasancewa wani ɓangare na yunƙurin Al-Sharaa na ƙarfafa gwamnatinsa da kuma tabbatar da cikakken iko kan hukumomin tsaron ƙasar.
Gwamnatin Syria ba ta bayyana cikakken dalilin sauye-sauyen ba, sai dai ta ce naɗin sabbin jami'an wani ɓangare ne na ci gaba da gyara da sabunta hukumomin tsaro na ƙasar.