An ceto wani ma’aikaci da ransa a ranar Lahadi bayan wata katangar shinge ta rufta a kansa yayin aikin rushe wani gini a Kofar Mata Zango, da ke Ƙaramar Hukumar Kano Municipal a Jihar Kano.Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, Sashen Ba da Agajin Gaggawa na hukumar ya samu kiran neman taimako da misalin ƙarfe 8:49 na safe daga wani Naziru Ahmad, wanda ya ba da rahoton aukuwar lamarin.
Nan take, jami’an kashe gobara daga hedikwatar hukumar suka isa wurin, inda suka tarar ana gudanar da aikin rushe wani gidan zama mai girman ƙafa 30 da 20.
Sanarwar ta bayyana cewa, yayin da ake ci gaba da aikin rushe ginin, katangar shingen ta fara karkacewa kafin daga bisani ta rufta, lamarin da ya rutsa da ɗaya daga cikin ma’aikatan, Sadiq Ahmad, yayin da yake ƙoƙarin tserewa.
“Jami’an cetonmu sun fara aikin ceto cikin gaggawa, inda suka samu nasarar ceto wanda abin ya shafa da ransa. Daga nan aka garzaya da shi zuwa Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammed, sannan aka miƙa shi ga ɗan’uwansa, Naziru Ahmad, domin ci gaba da samun kulawar likitoci,” in ji sanarwar.
Hukumar Kashe Gobara ta ce har yanzu ana gudanar da bincike domin gano musabbabin ruftawar katangar.
Ta kuma buƙaci mazauna jihar da ma’aikatan gine-gine su riƙa bin ƙa’idojin tsaro yayin ayyukan rushe gine-gine da na gine-gine gaba ɗaya, domin kauce wa irin waɗannan haɗurra da za a iya hana aukuwarsu.
“Mun yi kira ga al’umma da su kiyaye dukkan matakan tsaro yayin gudanar da ayyukan rushe gine-gine da na gine-gine domin gujewa haɗurran da za a iya kauce musu,” in ji sanarwar.