Peter Obi Ya Karrama Ranar Haihuwarsa Da Ba da Tallafin Naira Miliyan 10 Ga Asibitin St. Raphael


Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ba da tallafin Naira miliyan 10 ga Asibitin St. Raphael da ke Umueri a Jihar Anambra domin inganta ayyukan kiwon lafiya, yayin da yake bikin cika shekaru 65 da haihuwa. Ya ce ranar haihuwa ya kamata ta kasance lokaci na yi wa al'umma hidima, ba na shagulgula da son kai ba.

Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi domin murnar cika shekaru 65 da haihuwarsa. Ya ce ya fara ranar ne da halartar taron godiya na coci (Mass of Thanksgiving) a Onitsha, kafin ya kai ziyara asibitin da ke ƙaramar hukumar Anambra East.

Ya ce, bisa ga ƙudirinsa na mayar da ranar haihuwa lokaci na hidima ga jama'a maimakon nuna isa, ya bayar da tallafin Naira miliyan 10 domin taimaka wa asibitin wajen ci gaba da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al'umma.

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce zagayawa cikin asibitin da kuma ganawa da marasa lafiya ya sake tunasar da shi muhimmancin shugabanci mai cike da tausayi.

Ya ce ganin marasa lafiya a lokacin da suke cikin mawuyacin hali ya sake tuna masa da cewa dukkan mutane suna da daraja iri ɗaya. Ya ƙara da cewa wasu daga cikin masu karɓar magani ba su da ƙarfin biyan kuɗin jinyarsu, amma duk da haka sun cancanci tausayi, mutunci da kuma samun ingantaccen kulawar lafiya.

Obi ya bayyana cewa asibitoci da makarantu su ne manyan jari biyu da kowace al'umma za ta iya zubawa, domin asibitoci na ceton rayuka, yayin da makarantu ke gina makomar al'umma.

Ya kuma sanar da cewa zai shafe sauran kwanakin watan yana ziyartar makaranta ko asibiti guda, inda zai riƙa bayar da tallafi a matsayin nuna godiya ga Allah ta hanyar aikata alheri.

Ya ce, maimakon bikin da zai mayar da hankali a kansa, yana son bikin da zai fifita jin daɗin bil'adama.

Da yake yin tsokaci kan halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu, Obi ya ce ranar haihuwarsa ta zama lokaci na yin nazari mai zurfi kan halin ƙasar, ba na gudanar da manyan bukukuwa ba.

Ya ce duk da dimbin albarkatun ƙasa da na ɗan Adam da Najeriya take da su, miliyoyin 'yan ƙasa na ci gaba da fama da talauci, rashin aikin yi, matsalolin lafiya da ƙarancin damar rayuwa.

A cewarsa, bai dace mutane su riƙa yin shagulgula cikin almubazzaranci ba, alhali mutane da dama na fama da talauci, rashin lafiya, rashin aikin yi da ƙarancin damar samun ci gaba.

Obi ya ce ranar haihuwa ya kamata ta zama abin tunatarwa ga shugabanni da sauran jama'a game da alhakin da ke kansu na bayar da gudummawa wajen gina ƙasar da al'ummomi masu zuwa za su rayu cikin walwala.

Ya ƙara da cewa tsawon shekarunsa a harkokin kasuwanci da kuma hidimar gwamnati, ya kasance yana ƙin karɓar kyaututtuka masu tsada ko shirya bukukuwa na alfarma, yana ƙarfafa masu yi masa fatan alheri su karkatar da irin waɗannan kuɗaɗe zuwa ayyukan da za su amfani al'umma na dogon lokaci.

A cewarsa, hakan ya taimaka wajen gina makarantu, ɗakunan kwanan ɗalibai da sauran muhimman gine-ginen da suka amfani marasa galihu.

Obi ya bayyana cewa cika shekaru 65 ya ƙara tabbatar masa da cewa mafi girman nasarar rayuwa ba tarin dukiya ko lambobin yabo ba ne, sai dai irin kyakkyawan tasirin da mutum ya bari a rayuwar sauran mutane.

Post a Comment

Previous Post Next Post