Tinubu Ya Gargadi Gwamnoni Kan Gina Gadojin Sama Marasa Muhimmanci

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi da su daina gina gadojin sama (flyovers) a wuraren da ba su da cunkoson ababen hawa, yana mai cewa ya kamata su karkata karin kudaden da suke samu daga asusun tarayya wajen gina hanyoyi da za su inganta rayuwar al'umma tare da saukaka ayyukan jami'an tsaro.

Bola Ahmed Tinubu

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya na Jihar Oyo karkashin jagorancin Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja.

Shugaban ya ce jihohi na samun ninki hudu zuwa biyar na kudaden da suke karba a baya, yana mai cewa babu dalilin da zai sa a fifita gina flyovers a wuraren da ba su da bukata maimakon hanyoyin da za su kai ga yankunan karkara.

Har ila yau, Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta taba biyan kudin fansa ko yin sulhu da masu garkuwa da mutane ba. Ya ce waɗanda su ka sace dalibai da malamai a karamar hukumar Oriire ta Jihar Oyo sun bukaci a saki wasu mambobinsu da ke tsare tare da biyan kudin fansa, amma gwamnati ta yi watsi da bukatunsu.

Shugaban ya kuma bayyana cewa matakin kara yawan rundunonin Sojojin Najeriya daga guda takwas zuwa 12 na da nufin rage lokacin daukar matakin gaggawa da kuma karfafa yaki da ta'addanci da 'yan bindiga.

Tinubu ya kara da cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da shirye-shiryen kafa 'yan sandan jihohi tare da samar da dokokin da za su hana amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba, yana mai dora alhakin karuwar matsalar tsaro kan rikice-rikicen da ke faruwa a kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

Post a Comment

Previous Post Next Post