Rarara Ya Saki Dandanon Sabuwar Waka Mai Suna Malam Ya Yi Rawa Ba Wai Ba

A cikin daren yau Alhamis ne, shahararren mawaƙin siyasar nan kuma Sarkin mawaƙan ƙasar Hausa Dr. Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya saki Sabuwar wakar cin zarafi ga Malam Ali Isa Fantami ɗan takarar gwamnan Gombe a jam'iyyar PDP.

Mawaƙin ya yi amfani da salon da ya fi iyawa a waƙoƙinsa na zambo, inda ya zambaci Malam ɗin ta hanyar aikata shi da nuna shi a matsayin ɗan marisa, wato wanda ya sha ya bugu ya yi tatul.

Mawaƙin ya bayyana haka a cikin ɗanɗanon waƙar da ya saka wadda ba ta wuce sakanni arba'in ba zuwa minti ɗaya. A cikin waƙar ya bayyana wata waƙi'a ta zare idanu da Malam ya yi a wani lokacin taro da ya gabatar a baya.

Yadda abin ya faru, Malam ya cire gilashin fuskarsa sannan ya zazzaɓi idanu kana ya ce: "Kai da ganin waɗannan idanun, ka san na wuce a yi min barazana." Wannan abin da ya faru shi ne fa Rarara ya ɗauke shi ya juya har ma ya ƙirƙiri waƙar Malam Ya Yi Rawa Ba Wai Ba.

Daga sakin waƙar da ba a wuce mintina talatin ba, mutane sama da dubu biyu ne suka kalli ɗanɗanon waƙar, da yawansu kuma sun yi Allah wadai da wannan waƙar. Wadda al'umma suke ganin waƙa ce ta cin mutunci da taɓa janibin malanta. Wanda da yawan mabiyan Rarara sun fara bayyana barranta daga binsa saboda dalilin wannan waƙar, yayin da wasu kuma suka fara kofin Ala tsine da iƙirarin lallai ƙarshen Dauda ya zo, tun da har ya fara taɓa malanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post