Kulob din Real Madrid ya kammala ɗaukar matashin ɗan wasan gaba Carlos Espi daga Levante a ranar Alhamis kan kuɗin da aka ruwaito ya kai Yuro miliyan 25 (kimanin dala miliyan 29).
Matashin mai shekara 21 ya kasance yana jan hankalin wasu kulob din gasar Premier ta Ingila, amma zakarun Turai sau 15, Real Madrid, sun yi gaggawar kammala cinikin, yayin da ake sa ran Gonzalo Garcia zai koma Fulham.
A cikin wata sanarwa da kulob din ya fitar, ya ce, “Espi zai kasance tare da kulob dinmu na tsawon shekara biyar masu zuwa, har zuwa ranar 30 ga Yuni, 2031.”
Espi ya zura kwallaye 11 a gasar La Liga a kakar wasan da ta gabata cikin wasanni 25 da ya buga a matakin farko.
Shi ne ɗan wasa na biyar da Real Madrid ta ɗauka a wannan bazarar, bayan Marc Cucurella, Bernardo Silva, Ibrahima Konate da Denzel Dumfries.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai sun ce Real Madrid ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan gefe na Ivory Coast, Yan Diomande, daga RB Leipzig, yayin da ake kuma danganta ɗan wasan tsakiya na Manchester City, Rodri, da komawa kulob din.
Real Madrid, wadda ta naɗa gogaggen kocin Portugal Jose Mourinho domin maye gurbin Alvaro Arbeloa, na ci gaba da sake fasalin tawagarta bayan shafe kakar wasa biyu a jere ba tare da lashe wata babbar kambu ba.