Yakin Iran da Amurka na Son Dawowa Sabo Kan Mashigar Hormuz

DA ƊUMI-ƊUMI!! Rahotanni sun bayyana cewa Amurka ta ƙaddamar da jerin hare-hare da ta bayyana a matsayin masu ƙarfi kan Iran bayan wasu hare-hare da aka kai wa jiragen dakon mai na kasuwanci uku a Mashigin Hormuz.

Hukumar rundunar sojin Amurka, CENTCOM, ta ce manufar farmakin ita ce, Tehran ta gane kurenta kan hare-haren da ta kai kan wasu jiragen ruwa na kasuwanci a wannan yanki na ruwa na duniya.

A martanin da ta mayar, Iran din ta yi Allah-wadai da matakin sojan na Amurka, tana mai cewa hakan ya saba wa yarjejeniyar fahimtar juna da kasashen biyu suka sanya wa hannu a watan da ya gabata.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya yi gargadi cewa Tehran za ta dauki matakai masu tsauri domin mayar da martani.

Post a Comment

Previous Post Next Post