A Najeriya, gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin kasar ta gargadi al'ummar jihar game da yin sulhu da yanbindiga masu garkuwa da mutane.
Gwamnatin ta ce duk wanda ya yi sulhu da yanbindiga ya yi gaban kansa tare da nanata cewa ba za ta yi sulhu da yan fashin daji da suka addabi jihar ba.Gwamnatin ta kara jaddada hakan ne bayan wasu dattawa a yankin Maradun kusan 40 sun kubuta daga hannun yanbindiga bayan sun je yin sulhu da yanbindigan.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban karamar hukumar Talatar Mafara, Yahaya Abubakar Yari, ya ce: Sulhu ana yinsa ne da mutanen da misali suka yi tawaye saboda wasu bukatu nasu na neman 'yanci wanda hakan har ya kai su ga daukar makami.