Al'ummar duniya, musamman masu sha'awar kallon ƙwallon ƙafa sun yi Allah wadai da yadda hukumar ƙwallon ƙafa take nuna rashin goyon bayan ƙungiyoyin Afirka ta yadda duk yadda za su yi ƙoƙari sai sun yi yadda suka yi suka kwarfe su, don ganin darajarsu ba ta ɗaukaku kamar yadda suke ba, cece-ku-cen ya ɓarke ne bayan kammala wasan da aka yi tsakanin Argentina da Egypt wasan da aka tashi 3 da 2.
A wasan na jiya dai, wasan da aka fafata tsakanin Argentina (Shafaffu da mai) da kuma Egypt alƙalin wasan ƙuru-ƙuru ya bayyana ra'ayinsa ga waɗanda suke son yin nasara a wasan. Daga cikin abubuwan da suka bayyana hakan kuwa a alƙalancinsa akwai kashe ƙwallon da Egypt ya yi wanda ya kashe da cewa an yi wa Martinez ɗan bayan Argentina ƙeta, abu na biyu shi ne yadda ya ƙi hura fenariti a dukan da aka yi wa Salah a cikin da'irar ragar Argentina, wanda hakan ta kai ga Argentina har suka ci ƙwallon kuma ba a kashe ta ba. Da dai sauran ƙorafe-ƙorafe waɗanda suka sanya da yawan masu fashin baƙi akan al'amuran ƙwallon ƙafa suka yi Allah wadai.
Shi ma mai horar da ƙungiyar Hossam Hassan ba a bar shi a baya ba wajen tofa albarkacin bakinsa inda ya ce: "Da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ɗaukar kofin duniya kawai ta yi ta miƙa wa Argentina da ya fi a kan ta gayyato mu nan ta ɓata mana lokaci, kowa dai ya ga abin da ya faru, don haka mu mun san wannan kawai an yi mana fashin wasa ne, kuma dole sai na faɗa duk hukuncin da za su ɗauka su ɗauka bai dame ni ba."