Yan Bindiga Sun Kai Hari Cibiyar NIPSS A Jihar Plateau

Rahotanni daga jihar Plateau sun tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sake kai hari cibiyar horon ilimin dokoki da dabarun mulki ta ƙasa, wato National Institute for Policy and Strategic Studies da ke Kuru, kusa da Jos a jihar.

National Institute

Shugaban Sashen Hulɗa da Jama'a na cibiyar, Dr. Osime Samuel, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

A cewarsa, jami'an tsaro sun yi gaggawar mayar da martani, inda suka fafata da maharan a musayar wuta, lamarin da ya tilasta musu janyewa daga harin.

Ya ce an kashe ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin maharan ne yayin artabun, yayin da sauran suka tsere da raunuka daban-daban.

Samuel ya bayyana cewa maharan ba su samu nasarar kutsawa cikin harabar cibiyar ba, kuma dukkan mahalarta shirye-shirye, ma'aikata, mazauna cibiyar da kadarorinta suna cikin ƙoshin lafiya.

Ya kuma ce hukumomin tsaro sun ƙara tsaurara bincike domin kamo waɗanda suka tsere, tare da ƙarfafa sintiri da sauran matakan tsaro a ciki da wajen cibiyar.

A ranar 16 ga watan Yuni, wasu 'yan bindiga sun kai hari a NIPSS inda suka kashe jami'an tsaro uku. Wannan sabon hari na ƙara nuna kalubalen tsaro da cibiyar ke fuskanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post