Duka bayanan da suke a ƙasa gyararraki ne na ilimi cikin natsuwa da basira Malam AbdulRahman Musa Isma'il (AMI) ya lailayo wa Malam Jamilu wanda yake limanci a Masallacin Marigayi Dr Idris Abdul'aziz Dutsentanshi a karatunsa da ya gabata.
Kabada Sanarwar Ayi Maka Gyara Kuma Zaka karba Duk Ranar Laraba 10 to 11pm,To Amma Zai Iya yiwuwa mutum Bai Saurara Awannan Lokacin ba,
Shiyasa Nanemi Number dinka, Amma Sai aka Samu akasi Baka Dauka ba,Tun Daren jiya Haka Yauma Baka Dauka ba!.🤔
Sainaga Kyautuwar Sanar Maka tanan Amma Da kaɗauki Kiran Babu Buqatar yimaka Tanan😎
Faɗinka SAHEEHUL JAMIE Shine Sunan da AL-IMAMUL BUKHARIY yasanyawa Littafinsa suna❌
Domin Bukhariy Sunan Littafinsa Shine:الجامع المسند الصحيح المختصر من أمور رسول الله (ص)وسننه وأيامه ✅
MUSLIM MA HAKA❌
الجامع المسند الصحيح من السنن بنقل العدل عن العدل عن رسول الله (ص)
Shine Cikakken Sunan SAHEEHU MUSLIM ✅
Fadinka Duk Littafi سنن: Ana Nufin Littafin Dabai Taƙaita da'iya Saheehai ba❌
Ataƙaice Ana Nufin Littafin Da'aka Rubutashi Akan (أحاديث الأحكام)Littafin Daya Ƙunshi Hadeethan Hukunce-Hukunce ✅
Fadinka MUSNAD Littafin Da'aka Rubutashi ba Akan Mauduu'iy ba❌
Abunda Ake Nufi DA MUSNAD shine:Littafin Da'aka Rubutashi Akan Zubo Hadeethan kowanne Sahabiy Aguri Guda,kafin Atafi Zuwa Wani Sahabin✅
""(Makiyyyina Au madaniyyina) Wata mas'ala ce me Zaman Kanta Wannan""".
Fadinka AL-MUSANNAF kayi Ƙokari,Amma Abunda yakamata kace shine:An Tsara Shine Akan kawo Hadeethai DA Ãthãr Saheehai Ko Akasi Amma Baya Tarjeehin Masa'il Kaine Zakayi kokarin Yadda Zakayi Wajen TARJEEHI Tareda Kula DA Fiqhun Babi✅
FA'IDA:
Samun Littafi me Tahqeeqi Ba Yana Nufin Aje Akwanta Adogara daduk Abunda ya inganta ba, a'a, Kawai Amfanin Littafi me Tahqeeqi DA Takhreeji Shine,Sauƙaƙa Maka zuwa Inda SHAWAHEED Dakuma Zuwa GA MARAJI'U.Akula Dakyau.🥰
Fadinka SAYYIDUL HUFFAZ Shugaban Duk Wani AL-HAFIZ❌
Abunda yake Faruwa Ana Yiwa malamai IRIN wannan kirarin ne,Wajen Bayyana Iliminsu,Amma Iya Wannan Zamanin Nasu Ake Nufi✅
FA'IDA
Shiyasa Zakaga AZZABIY R.H. Kaga YAKAN CEWA MUTUM خاتمة الحفاظ Aiba Yana Nufin Baza'a Qara Samun Wani ba,Akula Dakyau🥰
Fadinka MUTTAHIM❌
Abunda zakace shine:MUTTAHAM✅
Fadinka FATAHUL MUGEETH Na IRAQIY❌
Alfiyyar ce Ta IRÃQIY Amma Shi FATAHUL MUGEETH ɗin Na SAKHAWIY ne✅
Fadinka أعلمهم IBNUL MADEENIY Wai Wanda Yafeesu Sanin Gundarin Hadeethin❌
Abunda Ake Nufi Shine Wanda Yafisu Sanin ILAL NA HADEETHIN✅
Fadinka WADA'AN LIKITABIN Ana Nufin Wanda Yafeesu Iya Rubuta Littafi❌
Abunda Ake Nufi Wanda Yafeesu kawowa DA tsagwaron Hadda Kamar Yana karantawa A Littafi✅
fadinka KITABUƊ DAHARA Haka yake Cikin MUSNAD❌
Littafin MUSNAD Babu Babi Kawai Iya Hadeethan yake zubowa,Amma Nafi Tunanin nan SUƁUTAR BAKI ne😎
Fadinka KAM YAMSAHU ALAL KHUFFAINI❌
KAM YUMSAHU ALAL KHUFFAINI✅
Fadinka SIRU A'ALÃMIN NUBALA❌
SIYARU A'ALÃMIN NUBALA ✅
Kaɗan Daga Abunda Zanyi tsokaci kai Kenan
Babu Ruwana da gyaran Larabci Wannan Iya Abunda yashafi Ɓangaren Hadeethi Daka Buqaci Ayi Maka Gyara ne,Idan Allah yasa Kagyara, To Babu Buqatar Adunga yimaka ta Social media,😏
AYI KARATU KAFIN KOMAI
~AMI
Tags
Labarai