Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Karamar Hukumar Bungudu A Zamfara Tare Da Kashe Jami'an Tsaro Hudu

Ana zargin wasu 'yan bindiga da sace shugaban karamar hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Bungudu, bayan kai hari gidansa da ke unguwar Zango a daren Alhamis.

Hon. Nura Umar Bungudu

Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin garin Bungudu tare da nufar gidan shugaban karamar hukumar, inda suka yi artabu da jami'an tsaro da ke gadin gidan.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Daily Trust cewa maharan sun kashe 'yansanda biyu da jami'an sintiri biyu kafin su yi awon gaba da shugaban karamar hukumar tare da wasu daga cikin iyalansa.

Majiyar ta ce jami'an tsaron sun yi ƙoƙarin dakile harin, amma makaman da maharan ke ɗauke da su sun fi ƙarfinsu. Ta ƙara da cewa an fara sace shugaban karamar hukumar tare da matarsa da 'ya'yansa, sai dai jami'an tsaro da suka bi sawun maharan sun samu nasarar ceto yara huɗu ko biyar daga cikinsu.

A cewar majiyar, duk da isowar ƙarin jami'an tsaro, sun isa ne bayan maharan sun riga sun tsere da shugaban karamar hukumar.

Ta kuma danganta yawaitar irin waɗannan hare-hare da makamai masu ƙarfi da 'yan bindigar ke amfani da su, tare da zargin akwai masu ba su bayanan sirri da ke taimaka musu gudanar da hare-haren.

Mazaunan yankin sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara matakan tsaro a Bungudu da sauran yankunan da ke fuskantar barazanar hare-haren 'yan bindiga domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar 'yansandan Jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba, domin ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post