'Yan bindiga sun sace Shugaban Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Alhaji Nura Abdullahi, bayan sun kai hari gidansa da sanyin safiyar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe jami'an tsaronsa hudu, da suka hada da 'yan sanda biyu da kuma jami'an sa-kai biyu, yayin da suke musayar wuta da masu kai harin.
Wani mazaunin Bungudu, Abdullahi Na Allah Said, ya ce 'yan bindigar sun shiga garin cikin adadi mai yawa, inda suka nufi gidan shugaban karamar hukumar kai tsaye. Ya bayyana cewa sun yi awon gaba da shugaban tare da matarsa da 'ya'yansa kafin su nufi daji.
A cewarsa, jami'an tsaron da ke gadin gidan sun yi kokarin dakile harin, amma ba su samu nasarar hana sace shugaban ba. Ya kara da cewa jami'an tsaro hudu sun rasa rayukansu a yayin artabun.
Sai dai rundunar Operation FANSAN YAMMA ta bayyana cewa dakarunta sun yi gaggawar isa wurin bayan jin karar harbe-harbe, inda suka gwabza fada da maharan.
A cikin wata sanarwa da Jami'in Yada Labarai na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar Asabar, ya ce matakin da sojojin suka dauka ya tilasta wa 'yan ta'addan barin mutum biyar daga cikin iyalan shugaban karamar hukumar.
Wadanda aka ceto sun hada da yara biyu, mahaifiyarsa, matarsa da kuma wani dan uwansa. Sai dai maharan sun tsere da shugaban karamar hukumar zuwa cikin daji.
Sanarwar ta ce harin ya yi sanadin mutuwar 'yan sanda biyu da jami'in sa-kai guda daya da ke cikin tawagar tsaron shugaban. Haka kuma wani farar hula ya rasa ransa, yayin da babban yayansa, Alhaji Bello Umar, ya samu raunuka.
Bayan faruwar lamarin, Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta kaddamar da wani gagarumin samame na hadin gwiwa tare da Rundunar 'Yan Sanda ta Najeriya, Hukumar DSS da kuma jami'an sa-kai domin gano maboyar maharan da ceto shugaban karamar hukumar.
Rundunar ta tabbatar da cewa tana amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen tabbatar da an kubutar da Alhaji Nura Abdullahi cikin koshin lafiya.
Har ila yau, ta bukaci al'ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, tare da bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen nasarar aikin ceto.