Rundunar 'Yan Sandan Jihar Sakkwato ta yi nasarar daƙile wani hari da ake zargin 'yan bindigar Lakurawa ne suka kai a Ƙaramar Hukumar Tangaza, inda ta kwato shanu 11 da aka sace tare da kama wasu
da ake zargi da hannu a fasa shaguna da satar babura a wasu ayyuka daban-daban da ta gudanar a faɗin jihar.Rundunar ta bayyana cewa jami'an ofishin 'yan sanda na Tangaza, da na Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane (Anti-Kidnapping Unit), Sashen Rage Laifuka a Ƙauyuka (Village Crime Reduction Unit – VCRU) da Strike Force ne suka gudanar da waɗannan ayyuka, wanda ke nuna ƙudirin rundunar na ci gaba da yaƙi da 'yan bindiga da masu aikata laifukan da suka shafi dukiyoyin al'umma.
A cikin wata sanarwa da Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar, Ahmad Rufa'i, ya fitar a ranar Talata, ya ce da yammacin ranar Litinin wasu da ake zargin 'yan bindigar Lakurawa ne suka mamaye ƙauyen Ayawa da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza, inda suka riƙa harbe-harbe ba tare da ƙa'ida ba kafin su yi awon gaba da shanu 11.
Rufa'i ya ce bayan samun kiran gaggawa daga mazauna yankin, DPO na Tangaza tare da jami'ansa, da haɗin gwiwar jami'an Anti-Kidnapping Unit da VCRU, sun garzaya wurin tare da rufe dukkan hanyoyin da maharan za su iya bi wajen tserewa.
Ya ce jami'an tsaron sun yi musayar wuta mai zafi da maharan na wani lokaci, amma saboda ƙwarewar jami'an da kuma ƙarfin makamansu, 'yan bindigar suka yi watsi da shanun da suka sace tare da tserewa zuwa cikin dajin da ke kusa.
Rundunar ta tabbatar da cewa an kwato dukkan shanun 11 lafiya, sannan aka mayar da su ga masu su.
A wani samame na daban, Strike Force ta kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a fasa wani shago a unguwar Guiwa Low Cost da ke cikin birnin Sakkwato.
Lamarin ya biyo bayan ƙorafin wani ɗan kasuwa mai suna Marwanu Akibu, wanda ya kai rahoton cewa wasu da ba a san ko su wanene ba sun fasa shagonsa a ranar 10 ga watan Yuli tare da sace yaduddukan atamfar mata guda 53.
Rufa'i ya ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, Mustapha Danbaba, yayin da jami'ai ke sintiri a yankin Old Market. A cewarsa, wanda ake zargin ya amsa laifin tare da bayyana cewa ya sayar da kayan ga wani mai suna Abubakar Usman, yayin da Bashar Abubakar da Sa'adu Shehu suka taimaka masa wajen sayar da kayan satar. Ya ce bincike kan lamarin na ci gaba.
Hakazalika, Strike Force ta kama wani da ake zargi mamba ne na ƙungiyar masu satar babura bayan mazauna unguwar Gidan Masau sun kai rahoton sace babura da dama a yankinsu.
Sanarwar ta ce wanda ake zargin, Kabiru Abubakar, ya amsa cewa shi da wani Ibrahim Muhammad, wanda har yanzu ake nema, suna haɗa baki wajen satar babura daga yankunan Mana Babba, Nakasari, Bado Quarters, Gidan Kanawa da Tamaje.
Binciken farko ya nuna cewa ana sayar da baburan da aka sace ga wasu mutane biyu da ake zargi masu sayen kayan sata ne, wato Ahmad na Sabon Titi da Kabiru na unguwar Hausawa, waɗanda suma jami'an tsaro ke ci gaba da nema.
Da yake yabawa jami'an da suka gudanar da waɗannan nasarori, Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Sakkwato, Hassan Shaffa, ya sake jaddada ƙudirin rundunar na kawar da masu aikata laifuka daga jihar.
Ya ce rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma, tare da yin kira ga mazauna jihar da su ci gaba da kasancewa masu sa ido da kuma bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da aikata laifuka.