Bayan Kammala wasannin gasar cin kofin duniya, cikin kwanaki da ba su wuce 21 ba, ''yan wasan da suka halarci gasar, za su yi hutunsu sannan su koma ƙungiyoyinsu domin fara wasannin sabuwar kaka ta 2026/2027 ga jadawalin yadda wasu wasannin za su dawo nan a ƙasa:
Wasannin gasar Carabao Cup Wanda ake yi a Ingila za a dawo nan da kwanaki 17
Sai gasar cin kofin EFL wanda shi ma ake yin sa a Ingila za a fara fafatawa nan da kwanaki 24
Gasar Premier League kuwa, kwanaki 31 ne suka saura domin a dawo a ci gaba da fafatawa, wadda ita ma gasar a Ingila ake dokata.
Ita kuwa fitacciyar gasar nan da ta shahara wato Gasar Cin Kofin Zakarun Turai (Champions League) akwai sauran kwanaki 49 daga yau kafin a fara gasar, gasa ce da ƙasashe 15 zuwa 18 ke samun wakilcin ƙungiyoyi 36 domin taka rawa a gasar.
Ita kuwa gasar cin kofin FA Cup za a fara doka rukunin 'yan uku (3rd round) nan da kwanaki 172.
Sai kuma gasar cin kofin Turawa na Euro da za a fafata nan da shekaru biyu masu zuwa 2028 wanda ƙididdiga ta nuna saura kwanaki 689.