Ƙasar Spain na iya rasa har zuwa kashi 30 cikin ɗari na kuɗin kyautar dala miliyan 50 da ta samu bayan lashe Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026, sakamakon dokokin harajin gwamnatin tarayyar Amurka.
Rahotanni sun bayyana cewa, bisa dokokin harajin Amurka, duk wani kuɗin shiga da aka samu daga ayyukan da aka gudanar a cikin ƙasar na iya kasancewa ƙarƙashin haraji.
Haka kuma, 'yan wasa da sauran baƙi da ba mazauna Amurka ba, waɗanda suka samu kuɗaɗen shiga daga wasanni da suka buga a ƙasar, ana iya cire musu harajin tarayya na kashi 30 cikin ɗari, sai dai idan wata yarjejeniyar haraji ko keɓancewa ta tanada akasin haka.
Spain ta zama zakarar gasar bayan ta doke Argentina da ci 1-0 a wasan ƙarshe da aka buga a filin wasa na New York New Jersey Stadium ranar Lahadi, 19 ga Yuli, 2026.
FIFA ta sanar cewa zakaran gasar zai karɓi dala miliyan 34 daga cikin jimillar kuɗin kyautar dala miliyan 871 da aka ware domin gasar mai ƙasashe 48.
Da yake martani kan yiwuwar wannan haraji, ɗan majalisar dokokin Amurka daga jam'iyyar Republican mai wakiltar jihar Tennessee, Tim Burchett, ya bayyana matakin a matsayin mai tsauri.
Ya ce, "Ina ganin wannan rashin adalci ne. Ban goyi bayansa ba, amma 'yan wasan Amurka ma suna biyan irin wannan haraji, don haka waɗanda suka zo nan sun san dokar tun kafin su zo."
Burchett ya ƙara da cewa, ɗora irin wannan haraji kan 'yan wasa na ƙasashen waje na iya aika saƙo mara kyau, musamman yayin da Amurka ke shirin karɓar manyan wasannin duniya a nan gaba.
Ya ce, "Ba ni da sha'awar yadda Hukumar Haraji ta IRS ke aiki. Muna son mutane su zo ƙasarmu su kashe kuɗinsu, amma daga baya sai mu cire musu babban kaso. Ya kamata mu samar da tsarin haraji mafi kyau."
A nasa bangaren, mashahurin mai sharhi a kafafen sada zumunta William Copus, wanda aka fi sani da The Feedski, ya bayyana cewa yawanci ƙasashen da ke karɓar bakuncin Gasar Kofin Duniya kan rattaba hannu kan yarjejeniyar keɓance haraji ga FIFA, ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashe da kuma 'yan wasa.
Sai dai ya ce Amurka ba ta yi hakan ba, sabanin ƙasashe irin su Afirka ta Kudu, Brazil, Rasha da Qatar.
A cewarsa, FIFA ta samu keɓancewar haraji ne kawai a matakin ƙungiyar da kuma hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashe, amma wannan bai shafi ɗaiɗaikun 'yan wasa, masu horarwa da jami'an tawaga ba.
Ya ƙara da cewa, baya ga harajin tarayya na kashi 30 cikin ɗari, jihohin da aka gudanar da wasanni kamar New Jersey da California na kuma karɓar nasu haraji.
New Jersey na karɓar haraji har zuwa kashi 10.75 cikin ɗari, yayin da California ke karɓar har zuwa kashi 13.3 cikin ɗari. Saboda haka, wasu 'yan wasa na iya biyan harajin da ya kai kusan kashi 40 cikin ɗari na kuɗin da suka samu daga gasar kafin ƙasashensu su karɓi nasu harajin.