Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ta bayyana cewa Najeriya na da isasshiyar baiwar 'yan wasa da za ta iya ba ta damar samun tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2030, amma ta ce dole ne ƙasar ta gina ingantaccen kuma tsayayyen tsarin gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa domin komawa babban gasar.
A cikin nazarin da ta wallafa a shafinta na intanet ranar Laraba, FIFA ta ce tawagar Super Eagles ta kai zagayen 'yan wasa 16 na ƙarshe a wasanni uku daga cikin sau shida da ta halarci Gasar Kofin Duniya, amma ta kasa samun gurbin shiga bugu biyu na baya-bayan nan.
Najeriya ta kai zagayen na 'yan wasa 16 a gasannin shekarun 1994, 1998 da 2014, sai dai ba ta samu tikitin shiga gasar ta 2018 da kuma ta 2026 ba.
A fafatawar neman gurbin shiga gasar 2026, Super Eagles ta zo ta biyu a rukunin C bayan Afirka ta Kudu a wasannin neman tikitin da CAF ta shirya, lamarin da ya ba ta damar zuwa mataki na biyu domin tantance ƙasashen Afirka da za su fafata a wasannin neman gurbi ta hanyar intercontinental play-offs.
Tawagar da Eric Chelle ke jagoranta ta doke Gabon da ci 4-1 bayan ƙarin lokaci, inda ta kai wasan ƙarshe na neman tikitin shiga gasar. Sai dai ta gaza tsallake Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo), bayan da ta sha kashi a bugun fenariti sakamakon kunnen doki 1-1.
Duk da wannan rashin nasara, FIFA ta jaddada cewa Najeriya na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa a Afirka saboda yawan hazikan 'yan wasan da take samarwa.
Hukumar ta bayyana cewa damar Najeriya ta komawa Gasar Kofin Duniya ta 2030 ba za ta ta'allaka ne kawai kan ƙwarewar 'yan wasanta ba, illa dai za ta dogara ne kan samar da ingantaccen, tsayayye kuma mai ɗorewa tsarin gudanarwa wanda zai tabbatar da samun sakamako mai kyau a kai a kai.
FIFA ta ce: “Super Eagles ta kai zagayen 'yan wasa 16 a rabin gasannin Kofin Duniya guda shida da ta halarta, wato a shekarun 1994, 1998 da 2014, amma ba ta samu damar shiga bugu biyu na baya ba.
“Najeriya ta zo ta biyu bayan Afirka ta Kudu a rukunin C na wasannin neman gurbin shiga gasar ta bana. Wannan ya ba ta damar zuwa mataki na biyu domin tantance waɗanda za su wakilci Afirka a wasannin intercontinental play-offs. Bayan ta doke Gabon da ci 4-1 bayan ƙarin lokaci, tawagar Eric Chelle ta fuskanci rashin nasara a hannun DR Congo bayan bugun fenariti sakamakon kunnen doki 1-1.
“Duk da haka, kasancewar Najeriya na da dimbin hazikan 'yan wasa, damar da take da ita na ci gaba da kasancewa babba. Don haka, samun tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2030 zai fi dogaro da samun tsayayyen tsarin gudanarwa mai ƙarfi fiye da ƙwarewar 'yan wasa kaɗai.”