Sarkin Iwo da ke jihar Osun, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya bukaci a daina danganta 'yanbindiga da addinin Musulunci, yana mai cewa masu aikata laifuka ba su da addini.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sarkin ya ce sanya rawani ko amfani da sunan Larabci ba ya tabbatar da cewa mutum Musulmi ne.
Ya kara da cewa 'yanbindiga ba sa gudanar da sallar Musulunci ko sauran ibadun da ake bukata ga Musulmi.
Ya kuma bayyana cewa harshen Larabci ba na Musulmi kadai ba ne, domin akwai mabiya sauran addinai da ke magana da shi a kasashen Larabawa.
Oba Akanbi ya ce rashin tsaro da ayyukan 'yanbindiga sakamakon gazawar gwamnatocin baya ne, ba addinin Musulunci ba. Haka kuma ya bukaci gwamnati ta dauki matakin doka kan masu amfani da kafafen sada zumunta wajen bata sunan Musulmi ta hanyar danganta addinin da ayyukan ta'addanci.
