A Daren Jiya Barayin Daji Sun Shiga Ƙauyen Gidan Tanko Sun Dauki Mutane Uku

A daren jiya Laraba 12/08/2026, ɓarayin daji sun yi shigar burtu a ƙauyen Gidan Tanko da ke ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina.

Ɓarayin dajin sun shiga garin ne da tsakar dare, a daidai lokacin da sawu ya ɗauke, kuma ruwan sama ya fara sauka. 

Mun samu rahoton cewa, ɓarayin ba su harbi kowa ba, sai dai sun yi nasarar yin awon gaba da wani matashi wanda shekarunsa za su tasamma arba'in da ake kira da Halliru da ɗansa. Halliru dai matashi ne mai fafutukar rayuwa, domin ba a sa shi a lissafin mai kuɗin ƙauyan nasu, amma duk da haka suka yi awon gaba da su da kuma wata budurwa mai suna Aliya.

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa, sun shiga ƙauyen ne salin alin ba tare da harbin wani ko wata ba. Wanda wannan ne ya nuna cewa da ma sun shiga ƙauyen ne kawai domin ɗaukar waɗannan mutane guda uku

Garin ya faru ne, jim kaɗan bayan wani hari da aka kai a kusa da ƙauyan na Gidan Tanko a ranar Litinin da dare, awani gari da ake kira Jama'a da ke yankin Kogari ta ƙaramar hukumar Matazu da ke Nijar Katsina, inda a wannan hari suka kashe wani magidanci a cikin gidansa tare da sace dabbobin da har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ba a samu adadinsu ba.

Allah ya kuɓutar da su, ya kawo mana zaman lafiya a ƙasarmu bakiɗaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post