A duk lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ta bai wa masu ɗauke da makamai damar ajiye makamansu da miƙa wuya, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce: me ya sa gwamnati ke ci gaba da bai wa waɗanda ake zargi da aikata munanan laifuka irin wannan dama?
A Najeriya, wannan tsari ba sabon abu ba ne. A baya dai an fi danganta tsarin karɓar ƴanbindigar da suka miƙa wuya da mayaƙan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, da kuma sauran ƙungiyoyi a wasu sassan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.Yanzu kuma rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa duk wata ƙungiyar da ke ɗauke da makamai a ko'ina cikin ƙasar da ta yanke shawarar ajiye makamanta za a karɓe ta.
A cikin 'yan shekarun nan, yankin Kudu maso Gabas ya fuskanci hare-hare da dama kan jami'an tsaro, cibiyoyin gwamnati da kuma fararen hula.