Mene Ne Makamin Nukiliya, Wane Tasiri Yake Da Shi

Makamin Nukiliya (Nuclear weapon), wani nau'in makami ne mai matukar hatsari da kuma saurin fashewa sanadiyar wasu sinadaran kimiyya masu tarwatsewa da haifar da makamashin madda (atomic energy) a yanayin hayaki ko haske mai dauke da tururin guba ga lafiya da rayuwar bil'adama da muhallin shi.

Nukiliya

An tabbatar da cewa a duk lokacin da makamin ya fashe a wuri ko gari to lallai ne a sami karar fashewa mai tsananin firgitarwa wacce ke biye da hayaki mai dauke da guba tare da wuta mai ci balbal da haske mai matukar cutarwa muddin ya hadu da maddar muhalli. Wannan tururin hasken mai matukar cutarwa masana a fannin kimiyya sun bayyana cewa muddin aka sami fashewar wannan gubar a wuri, to ya na daukan shekara da shekaru ya na illata al'umma da duk nau'ukan ababe masu rayuwa (bil'adama ko dabbobi) a daukacin yankin. Masana sun bayyana wannan gubar da suna "radioactive radiation".

An bayyana cewa idan mizanin wannan makamin ya kai tan miliyan a misali, karfin fashewar shi na iya haddasa yar karamar girgizar kasa a wurin da ya auku. Manyan sinadaran kimiyyar da ake amfani da su wajen hada wannan makamin a duniya su ne; makamashin fulutoniyon (plutonium) da kuma yuraniyon (uranium). Ana gauraya su ne kuma a dafa su har sai sun kai mizani na zafi wanda ke canza asalin hakikaninsu zuwa wasu maddodin dabam, ya kuma basu tasirin fashewa ko hadewa da juna, sanadiyyar alakarsu ko kusancinsu da wasu makamashin haske ko maddodin dabam.

Saboda tsananin tasirinsa ga muhalli, tan guda na makamashin nukiliya da ke dauke cikin makami ko kwansonsa, idan aka harba shi, tasirin fashewa da kara da yawan sinadaran da zai fitar, daidai yake da tasirin fasa bam irin na zamani guda biliyan daya, a lokaci daya, kuma a wuri daya. Idan kuma aka samu fashewar makamin nukiliya da mizaninsa ya kai tan dubu ko sama da haka, to ya na iya konawa da kuma tarwatsa birni ko yanki mafi girma a duniyar yau. Sanadiyar tasirin da wannan makamin ya ke da shi ake masa lakabi da makamin-kare-dangi (weapon of mass destruction).

Kawo yanzun dai an tabbatar da akwai kasashe a kalla 9 wadaanda ke da wannan makamin a duniya, in da ake kiyasin cewa, kasar Rasha (Russia) ita tafi ko wace kasa yawan makaman a duniya, sai kuma kasar Amurka wacce take biye mata, sai kasar Faransa, sai kuma kasar Burtaniya, sai kasar Sin, (China) sai kasar Isra' ila, sai kasar Indiya, sai kasar Pakistan, sai kuma kasar Koriya ta Arewa.

Masana a fannin kimiyyar makamai sun bayyana cewa, kawo yanzun akwai nau'ukan makamin nukiliya guda biyu, shahararru, wadanda dukkan wasu nau'uka suka dogara gare su. Nau'i na farko shi ne nau'in da ke dauke da makamashin madda mai karfi, wanda ke tarwatsa juna ta hanyar warwatsuwar da suke yi yayin da aka harba su ta hanyar makamin da suke dauke cikinsu. Akan jejjera wadannan makamai masu gaggawar tarwatsewa ne waje daya, cikin kwanso ko makami guda kenan, sannan a harba su zuwa inda ake hari.

Wannan tsari tsohon yayi kenan, kuma shi ake kira da suna "the gun method", domin akan harba makamin ne kamar yadda ake harba harsashi da ke cikin bindiga. Ko kuma, a daya bangaren, a jera makamai masu dauke da makamashin fulutoniyon a wuri daya, cikin kwanso daya, da zarar an harba su, sai su harhade da juna, sannan su fashe. Wannan tsari shi ake kira da suna "the implosion method,"kuma shi ya kunshi nau’in farko na makamin nukiliya mai suna "Atomic Bomb", ko kuma "A Bomb".

Irin wannan nau’in ne kasar Amurka ta jefawa mutanen Japan a manyan biranensu, Na Hiroshima da Nagasaki A Ranakun 6 da 9 A watan Agusta 1945, a karshen yakin duniya na biyu, kamar yadda bayanai suka gabata a sama. Sai kuma nau’i na biyu kuma, wanda ke haifar da makamashin guba mai dimbin yawa sanadiyyar hadewar sinadaran madda masu tarwatsewa irin wanda ke dauke cikin nau’in farko, da kuma wasu sinadaran madda masu hadewa kafin su tarwatse.

Yadda ake 'kera wannan nau’in shine a na shigar da sinadaran madda masu tarwatsewa cikin ma’adana daya mai dauke da makamashin tururin haske, a gefensu kuma a jejjera sinadaran makamashi masu gamewa da juna lokacin fashewarsu irin su "tritium" da kuma "deuterium," ko kuma "lithium denteride", duk cikin kwanso ko ma'adana guda. Da zarar an jefa wannan makami a wurin da ake hari, sai wadannan sinadarai masu saurin tarwatsewa su tarwatse cikin ma’adanar.

Tarwatsewarsu ke haifar da haske mai tsanani nau’in "Gamma-ray" da kuma "X-ray," nan take sai wannan haske ya narka sinadaran "lithium denteride", ya tafasa su matukar tafasawa. Suna gama tafasuwa sai kawai su haifar da sinadarai nau’in neutron, masu gamewa da makamashin yuraniyon don haddasa fashewa da kara mai tsanani. Wannan nau’i kuma shi ake kira "Hydrogen Bomb," ko "H-Bomb", ko "Fusion Bomb", ko kuma "Thermonuclear Bomb."

Mallakar makamin kare-dangin ko makamin nukiliya dai shi ya mamaye lamuran manyan kasashen duniya, musamman irin su kasar Amurka. Kasar Koriya ta Arewa da kasar Farisa ko Iran wadanda ke fama da barazana daga manyan kasashen duniya bisa niyar su na mallakar makamin. 

An yi amfani da wadannan makamai a karon farko a lokacin yakin duniya na biyu wato makaman nan da Amurka ta yi amfani da su a biranen Hiroshima da Nagazaki na kasar Japan, da suka haddasa asara dubunan rayuka.

Bayan Amurka ta yi amfani da wadannan makamai sai suma sauran kasashe duniya hasali ma Rasha babar abokiyar adawar Amurka ta samu Fasahar kirkiro da wannan miyagun makamai, sannu a hankali sauran kasashen Turai kamar su Faransa, Jamus Birtaniya suma suka fara mallakar Nasu.

Ganin yadda yaduwar wannan makamai zai iya hadasa mumunan yaki a duniya sai shugaban kasar Amurka Eisenhower ya gabatar da wani jawabin a Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bada shawarar kirkiro wata hukuma da za ta haramtawa kasashen duniya mallakar makamai masu guba. Wannan shawara ta samu karbuwa.

Bayan da kasashe fiye Da 80 suka rattaba mata hannu sai a ka kirkiro wata Hukuma da aka dorawa nauyin  yaki da yaduwar makaman nukiliya wato IAEA, Hukumar mai cibiyarta a birnin Vienna na kasar Austriya ta fara aiki gadan-gadan ranar 29 ga watan July na 1957.

Bayan da ta kamata aiki sai hukumar  IAEA ta cigaba da jawo kasashe daban-daban na duniya wanda ba su rattaba hannu kan yarjejeniyar ba, da su gaggauta amincewa da ita, ta haka a cimma sabuwar yarjejeniyar wadda ita itama aka rada mata suna yarjejeniya hana yaduwar makaman nukiliya a shekara 1968.

Kasashen duniya da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.

Mafi yawan kasashen duniya sun rattabba hannu kan wannan yarjejeniya, wanda ba su sa mata hannu ba ba su wuce kasashe uku ba wato Indiya, Israel, da Paksitan, wanda su kam hanzu haka sun mallaki wannan makamai, amma kuma kawai kasar Koriya ta Arewa wadda ita a lokacin ta aka bullo da yarjeniyar ta sa mata hannu amma ta fita a watan Janairu na shekara 2003. 

Hukumomin Pyong yangh suka ce ba za su yarda ayi masu sakiyar da babu ruwa ba domin akwai kasashen da suke basu ga maciji da su wanda suka mallaki wannan makami a asirce saboda haka suma ya zama tilas su sami nasu domin kare kansu. Saboda haka ne tun daga wannan shekara har yanzu ake ta takkadama game da makamin nukiliya Koriya ta Arewa.

Banda Koriya ta Arewa wanda ita ta fito karara ta janye daga yarjejeniyar akwai kuma wasu kasashe kamar Uku wanda ba su janye ba amma a asirce suke aiki domin mallakar makamai na nukiliya.

Ta dayansu ne itace kasar Iran, wadda itama ake ta kai ruwa rana kan wannan batu, kasar Iran da Isra'ila na cikin zaman gaba to Isra'ila ce ma ba ta sa hannun ba kan yarejeniya hana yaduwar makaman nukiliya saboda haka ta mallaki su ba lefi ba ne, to ita Iran a zahiri ba ta fito fili ta ce ta mallaki wannan makami ba amma ana zargin ta da fakewa da guzuma domin ta harbi karsana wato hukumomin Tehran suna fakewa da shirin makamashin Nukiliya domin mallakar makaman nukiliya.

Bayan su, akwai kasar Libiya zamanin mulki marigayi Mu'ammar  Kaddafi, wadda ita ma a asirce ta shiga yunkurin mallakar makaman kare dangi, amma daga bisani ta lashe amanta, haka zalika Irak an yi mata wannan zargi, idan ma ba a manta ba, dalili da haka ne, Amurka ta kaddamar da yakin Irak, wanda ya kifar da mulkin shugaba Saddam Husain.

Bambancin Makamashin nukiliya da makamin nukiliya

Akwai bambanci tsakanin makamashin nukiliya da makamin nukiliya, kusan dukkan manyan kasashe masu cigaban masana'antu sun mallaki tashoshin samar da makamashin nukiliya wanda shi aikinsa shi ne wadatar da kasashen da wutar lantarki ta hanyar sarafa karafen Uranium.

Mun ga misali da bala'in da ya faru a tashar samar da makamashin nukiliya ta Fukushima a kasar Japan a shekarar 2011 sannan kamin ita akwai bala'in da ya faru a tashar samar da makashin nukiliya ta Cerbobyl a kasar Ukraine a watan Afrilu na shekara 1986, wanda sanadiyar sa dubbunan jama'a suka rasa rayuka sannan a yanzu haka mutanen da suka shaki gubar suke fama da matsalolin lafiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post