Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya buƙaci masu zaɓe su yi watsi da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a safiyar Alhamis, Adeleke ya yi gargaɗin cewa idan APC ta dawo mulki, za a iya komawa irin wahalhalun da ma’aikatan gwamnati suka fuskanta a baya, ciki har da biyan rabin albashi da matsalar ƙarancin abinci.
Adeleke, wanda yanzu yake takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar Accord Party bayan ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bayyana zaɓen gwamnan da ke tafe a matsayin zaɓi tsakanin ci gaban da gwamnatinsa ke ikirarin samarwa da kuma manufofin tsohuwar gwamnatin APC da yake zargin sun jefa talauci cikin al’umma.
Ya ce dole ne al’ummar Osun su yi amfani da ƙuri’arsu wajen kare abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da aka samu a ƙarƙashin gwamnatinsa, yana mai jaddada cewa “ba za mu taɓa komawa waɗancan kwanakin baƙi na APC ba.”