“Mutane suna ihu… na ga ƙura tana tashi daga gine-ginen maƙwabta, yayin da tubalan bango ke faɗowa,” in ji Angélica Ávila, bayan da wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.4 ta afka wa ƙasar Colombia, ta haddasa mummunar asara da hasarar rayuka.
Girgizar ta auku ne da ƙarfe 7:34 na safiyar ranar Litinin, 10 ga Agusta, a lardin Chocó, a zurfin kilomita 103, kamar yadda Hukumar Kula da Yanayin Ƙasa ta Colombia ta bayyana. An ji girgizar a faɗin yammacin ƙasar, har zuwa daruruwan mil.
Ya zuwa yanzu, mutane 132 sun rasu sakamakon girgizar, yayin da ake fargabar adadin zai ƙaru, domin jami’an ceto na ci gaba da tono baraguzan gine-gine da hannu da bokiti domin neman waɗanda suka tsira.
Shugaban ƙasar Colombia, Abelardo De La Espriella, wanda aka rantsar da shi kwanaki kaɗan kafin aukuwar wannan bala’i, ya ayyana dokar ta-baci a ƙasar.
Ya ce, “Ina so in tabbatar wa ’yan Colombia da ke cikin wannan hali mai wahala cewa ba su kaɗai ba ne. Suna da shugaban ƙasa da ke matuƙar damuwa da rayuwarsu, kuma zai yi duk abin da ya dace domin kare su, tallafa musu, tare da sake gina yankunan da bala’in ya shafa.”
Yaushe kuma a ina girgizar ta auku?
Girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.4 ta afku da ƙarfe 7:34 na safiya agogon ƙasar, inda cibiyar girgizar ta kasance a San José del Palmar, wani ƙauye mai kusan mutane 4,800 a yankin Chocó.
Bayan girgizar ta farko, an sake samun wasu ƙananan girgizar ƙasa guda biyu masu ƙarfin maki 2.8 da 4.8.
An ji girgizar har zuwa Bogotá, babban birnin ƙasar da ke nisan kusan mil 150 daga cibiyar girgizar. Ƙararrawar gaggawa ta yi ƙara, lamarin da ya sa mazauna birnin suka fice daga gine-ginensu domin tsira. Haka kuma an ji girgizar a ƙasashen Venezuela, Ecuador da Panama.
Yaya ƙarfin girgizar ya kasance?
Hukumar Kula da Yanayin Ƙasa ta Colombia ta ce girgizar ta kai maki 7.4 kuma ta faru a zurfin kilomita 103.
Masana sun bayyana cewa wannan ita ce girgizar ƙasa mafi ƙarfi da aka taɓa rubutawa a Colombia a ƙarni na 21. Masana daga Hukumar Nazarin Ƙasa ta Amurka (USGS) sun yi hasashen cewa girgizar ta samo asali ne daga motsin wani babban layin ɓarna (fault) da ke cikin farantin ƙasa na Nazca.
Masana sun kuma bayyana cewa kasancewar Colombia a mahadar manyan farantan ƙasa da dama yana sa ƙasar fuskantar girgizar ƙasa mai ƙarfi akai-akai.
Rahoton BBC ya nuna cewa tun daga shekarar 1950, sama da mutane 3,500 suka mutu sakamakon girgizar ƙasa a Colombia. Mafi muni daga cikinsu ya faru ne a shekarar 1999, lokacin da wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.2 ta afka wa yankin Coffee Region, inda ta yi sanadin mutuwar mutane 1,185.