Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka da Isra'ila sun amince su dakatar da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Iran, matuƙar an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin cikin gaggawa.
Trump ya ce ya yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa da Yarima mai jiran gadon Saudiyya, Mohammed bin Salman, da kuma bayan Iran ta tattauna da Saudiyya, Pakistan da Turkiyya domin rage tashin hankali a yankin.
Sai dai Iran ta musanta ikirarin cewa ta roƙi Amurka ta dakatar da hare-hare, tana mai cewa kalaman Trump ƙarya ne, tare da jaddada cewa dakarunta suna cikin shirin ko-ta-kwana.
Trump ya ce duk wata yarjejeniya dole ta haɗa da buɗe mashigar ruwa ta Hormuz gaba ɗaya da kuma dakatar da shirin nukiliyar Iran, yayin da rikicin ya ci gaba da haifar da tashin farashin mai da fargabar ƙarin rikici a Gabas ta Tsakiya.
